Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Warfare of Saints

107 ayoyi · 73 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka nake jure kome saboda zaɓaɓɓu, domin su ma su sami ceton da yake cikin Kiristi Yesu, tare da madawwamiyar ɗaukaka.

  2. Amma Ubangiji ya tsaya tare da ni, ya kuma ba ni ƙarfi, don ta wurina a yi cikakkiyar shelar saƙon har Al’ummai duka su ji. Aka kuma cece ni daga bakin zaki.

  3. Ubangiji zai cece ni daga kowane mugun hari yă kuma kai ni mulkinsa na sama lafiya. A gare shi ɗaukaka ta tabbata har abada abadin. Amin.

  4. Ta wurin kawo ’ya’ya masu yawa zuwa ga ɗaukaka, ya dace cewa Allah, wanda dominsa da kuma ta wurinsa ne kome yake kasancewa, ya sa tushen cetonsu yă zama cikakke ta wurin shan wahala.

  5. Da yake ’ya’yan suna da nama da jini, shi ma sai ya ɗauki kamanninsu na mutum domin ta wurin mutuwarsa yă hallaka wanda yake riƙe da ikon mutuwa, wato, Iblis

  6. ya kuma ’yantar da waɗanda dukan rayuwarsu tsoron mutuwa ya riƙe su cikin bauta.

  7. Bari mu tsaya da ƙarfi a kan ga begen da muka ce namu ne, gama shi da ya yi alkawarin, mai aminci ne.

  8. waɗanda ta wurin bangaskiya ne suka ci nasara a kan mulkoki, suka aikata adalci, suka kuma sami abin da aka yi alkawari; waɗanda suka rurrufe bakunan zakoki,

  9. suka kashe harshen wuta, suka kuma tsere wa kaifin takobi; waɗanda aka mai da rashin ƙarfinsu ya zama ƙarfi; waɗanda suka yi jaruntaka wajen yaƙi suka kuma fatattaki mayaƙan waɗansu ƙasashe.

  10. Mata suka karɓi ƙaunatattunsu da aka sāke tasar daga matattu. Aka azabtar da yawancin mutanen nan, amma suka ƙi a sake su, domin sun tabbata za su sami lada mafi kyau sa’ad da aka tā da matattu.

  11. Waɗansu suka sha ba’a da bulala, har da dauri da sarƙa, da kuma jefa su cikin kurkuku.

  12. Aka jajjefe su da duwatsu; aka raba su biyu da zarto; aka kashe su da takobi. Suka yi ta yawo saye da fatun tumaki da na awaki, suka yi zaman rashi, suka sha tsanani da kuma wulaƙanci

  13. Saboda haka, ku miƙa kanku ga Allah. Ku yi tsayayya da Iblis, zai kuwa guje ku.

  14. Abokaina ƙaunatattu, ina roƙonku, a matsayin bare da kuma baƙi a duniya, ku rabu da sha’awace-sha’awacen zunubin da suke yaƙi da ranku.

  15. Ku zama masu kamunkai, ku kuma zauna a faɗake. Abokin gābanku, Iblis yana kewayewa kamar zaki mai ruri, yana neman wanda zai cinye.

  16. Ku yi tsayayya da shi, kuna tsayawa daram cikin bangaskiya, domin kun san cewa ’yan’uwanku ko’ina a duniya suna shan irin wahalolin nan.

  17. Ina rubuta muku, ’ya’yana ƙaunatattu, domin kun san Uba. Ina rubuta muku, ubanni, domin kun san shi wanda yake tun farko. Ina rubuta muku, samari, domin kuna da ƙarfi, maganar Allah kuwa tana zaune a cikinku, kun kuma ci nasara a kan mugun nan.

  18. Ku, ’ya’yana ƙaunatattu, ku daga Allah ne, kun kuma yi nasara a kan magabtan Kiristi, domin wanda yake a cikinku ya fi wanda yake a duniya girma.

  19. domin duk haifaffe na Allah yana cin nasara a kan duniya. Bangaskiyarmu kuwa ita ce ta ba mu wannan nasara a kan duniya.

  20. Wa ya cin nasara a kan duniya? Sai wanda ya gaskata cewa Yesu Ɗan Allah ne.

  21. Abokaina ƙaunatattu, ko da yake na yi marmari ƙwarai in rubuta muku game da ceton nan namu, sai na ga ya dace in rubuta, in gargaɗe ku ku tsaya da ƙarfi cikin bangaskiya wadda aka danƙa wa mutane masu tsarki na Allah sau ɗaya tak.

  22. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara, zan ba shi ikon ci daga itacen rai, da yake cikin aljannar Allah.

  23. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara mutuwa ta biyu ba za tă cuce shi ba ko kaɗan.

  24. Duk mai kunnen ji, yă ji abin da Ruhu yake faɗa wa ikkilisiyoyi. Duk wanda ya ci nasara zan ba shi kaɗan daga cikin ɓoyayyiyar Manna. Zan kuma ba shi farin dutse tare da sabon suna a rubuce a bisansa, sananne kawai ga mai karɓan dutsen.

  25. Gare shi wanda ya ci nasara ya kuma aikata nufina har ƙarshe, zan ba shi iko a kan al’ummai.