Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Trees

132 ayoyi · 87 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai sassare itatuwan jeji da gatari har ƙasa; Lebanon zai fāɗi a gaban Mai Iko.

  2. Toho zai fito daga kututturen Yesse; daga saiwarsa Reshe zai ba da ’ya’ya.

  3. Amma an jefar da kabarinka kamar reshen da aka ƙi; an rufe ka da waɗanda aka kashe, tare da waɗanda aka soke da takobi, waɗanda suka gangara zuwa duwatsun rami. Kamar gawar da aka tattake da ƙafa,

  4. Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.

  5. Zan sa a hamada ta tsiro da al’ul da itacen ƙirya, da itacen ci-zaƙi, da zaitun. Zan sa itace mai girma a ƙasashe masu sanyi ya tsiro a ƙeƙasasshiyar ƙasa, tare da fir da kuma saifires,

  6. Za su tsiro kamar ciyawa a wuriyar ruwa, kamar kurmi kusa da rafuffuka masu gudu.

  7. Yakan ka da itacen saifires, ko kuwa ya ɗauki saifires ko oak. Yă bar shi yă yi girma a cikin itatuwan kurmi, ko yă shuka itacen fir, ruwan sama kuma yă sa yă yi girma.

  8. Abin hura wutar mutum ne; yakan ɗebi waɗansu yă hura wuta don yă ji ɗumi, ya hura wuta yă gasa burodi. Amma yakan ƙera zinariya yă kuma yi masa sujada; yakan yi gunki sa’an nan yă rusuna masa.

  9. Rabin katakon yakan ƙone a wuta; a kansa yakan dafa abincinsa, yă gasa namansa yă kuma ci sai ya ƙoshi. Yakan ji ɗumi yă kuma ce, “Aha! Na ji ɗumi; na gan wutar.”

  10. Da sauran itacen yakan yi allah, gunkinsa; yă rusuna masa yă kuma yi sujada. Yakan yi masa addu’a yă ce, “Ka cece ni; kai ne allahna.”

  11. Ba wanda yakan dakata ya yi tunani, ba wanda yake da sani ko fahimi ya ce, “Da rabinsa na yi amfani da shi don hura wuta; na ma gasa burodi a kan garwashinsa, na gasa nama na kuma ci. Ya kamata in yi abin ƙyama daga abin da ya rage? Ya kamata in rusuna wa guntun katako?”

  12. A maimakon sarƙaƙƙiya, itacen fir ne zai tsiro, a maimakon ƙayayyuwa kuma, itacen ci-zaƙi ne zai tsiro. Wannan zai zama matuni na abin da Ni Ubangiji na yi, madawwamiyar alama ce, wadda ba za a datse ba.”

  13. Kada baƙon da ya miƙa kansa ga Ubangiji ya ce, “Ai Ubangiji zai ware ni daga mutanensa.” Kada kuma wani bābā ya yi gunaguni cewa, “Ni busasshen itace ne kawai.”

  14. in tanada wa waɗanda suke baƙin ciki a Sihiyona, in maido musu rawani mai kyau a maimako na toka, man murna a maimako na makoki, da kuma rigar yabo a maimako na ruhun fid da zuciya. Za a ce da su itatuwan oak na adalci, shukin Ubangiji don bayyana darajarsa.

  15. Ba za su ƙara gina gidaje waɗansu kuma su zauna a cikinsu ba, ko su yi shuki waɗansu kuma su ci ba. Gama kamar yadda kwanakin itace suke, haka kwanakin mutanena za su kasance; zaɓaɓɓuna za su daɗe suna jin daɗin ayyukan hannuwansu.

  16. Maganar Ubangiji ta zo mini cewa, “Me ka gani, Irmiya?” Sai na amsa na ce, “Na ga reshen itacen almon.”

  17. Ga abin da Ubangiji Maɗaukaki yana cewa, “Ku sassare itatuwan ku tula ƙasa kewaye da Urushalima. Dole a hukunta wannan birni; saboda ya cika da zalunci.

  18. Har ’ya’yansu ma sun tuna bagadansu da ginshiƙan Asheransu kusa da itatuwa masu duhuwa da kuma a kan tuddai masu tsayi.

  19. Za su zama kamar itacen da aka dasa kusa da ruwa wanda ya miƙa saiwoyinsa zuwa cikin rafi. Ba ya jin tsoro sa’ad da zafi ya zo; ganyayensa kullum kore suke. Ba shi da damuwa a shekarar fări ba ya taɓa fasa ba da ’ya’ya.”

  20. “Ɗan mutum, da me itacen kuringa ya fi reshen waɗansu itatuwa kyau a cikin kurmi?

  21. Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa babbar gaggafa mai manyan fikafikai, dogayen gasusuwa da gasusuwa da yawa masu launi iri-iri ta zo Lebanon. Ta cire kan al’ul,

  22. “ ‘Ta ɗebi waɗansu irin ƙasarku ta sa a ƙasa mai taƙi. Ta shuka shi kamar itacen wardi kusa da ruwa mai yawa,

  23. Dukan itatuwan jeji za su san cewa Ni Ubangiji ne mai sa manyan itatuwa su zama ƙanana in kuma sa ƙananan itatuwa su zama manya. Nakan sa ɗanyen itace ya bushe, busasshen itace kuma ya zama ɗanye. “ ‘Ni Ubangiji na faɗa, zan kuma aikata.’ ”

  24. Yana da girma a kyau, da dogayen rassansa da ya baza, gama saiwoyinsa sun nutse can ƙasa har cikin yalwar ruwaye.

  25. Al’ul a cikin lambun Allah ba su kai shi ba, balle itatuwan kasharina su kai rassansa, ko itatuwan durumi su kai rassansa, ko itace a lambun Allah ya kai kyansa.