Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Trees: Juniper
Ayoyi game da Juniper
Shi kuma ya yi tafiya yini guda zuwa cikin hamada. Ya zo wurin wani itacen tsintsiya, ya zauna a ƙarƙashinsa, ya roƙa yă mutu. Ya ce, “Ya ishe ni haka, Ubangiji, ka ɗauki raina; ban fi kakannina ba.”
Sa’an nan ya kwanta a ƙarƙashin itacen ya yi barci. Farat ɗaya sai wani mala’ika ya taɓa shi, ya ce, “Tashi ka ci abinci.”