Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Titles and Names of Saints

122 ayoyi · 81 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai ya ce, “Zo, ya kai mai albarka na Ubangiji, don me kake tsaye a waje? Gama na shirya gida da wuri domin raƙuma.”

  2. cewa ba za ka cuce mu ba, kamar yadda ba mu fitine ka ba, amma muka yi maka kirki, muka kuma sallame ka cikin salama. Yanzu kuwa kai albarkatacce ne na Ubangiji.”

  3. Yanzu, in kuka yi mini cikakken biyayya, kuka kuma kiyaye yarjejjeniyata, to, za ku zama keɓeɓɓiyar taska a gare ni a cikin dukan al’ummai. Ko da yake duk duniya tawa ce,

  4. za ku zama firistoci masu tsarki da kuma al’umma keɓaɓɓiya a gare ni.’ Waɗannan su ne kalmomin da za ka faɗa wa Isra’ilawa.”

  5. “ ‘Kada a sayar da gona ɗinɗinɗin, gama ƙasar tawa ce, ku kuwa baƙi ne kawai, kuma ’yan haya nawa.

  6. Ku ’ya’yan Ubangiji Allahnku ne. Kada ku yi wa kanku zāne, ko ku yi wa kanku aski irin da akan bar sanƙo, saboda wanda ya mutu,

  7. gama ku jama’a ce mai tsarki ga Ubangiji Allahnku. Daga dukan mutane a fuskar duniya, Ubangiji ya zaɓe ku, ku zama abin mallakarsa.

  8. Ya furta cewa zai sa ku zama masu yabo, masu suna, masu daraja, fiye da dukan al’umman da ya yi. Za ku zama jama’a tsattsarka ta Ubangiji Allahnku, kamar yadda ya yi alkawari.

  9. Wannan ita ce albarkar da Musa mutumin Allah ya furta a kan Isra’ilawa, kafin yă rasu.

  10. Kai mai albarka ne, ya Isra’ila! Wane ne yake kamar ka, mutanen da Ubangiji ya ceta? Shi ne mafakarka da mai taimakonka da kuma takobinka mai ɗaukaka. Abokan gābanka za su zo neman jinƙai a gabanka, za ka kuwa tattake masujadansu.”

  11. Ya ku zuriyar Isra’ila bayinsa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub maza, zaɓaɓɓunsa.

  12. Ya Allahnmu, ba kai ba ne ka kore mazaunan wannan ƙasa a gaban mutanenka Isra’ila ka kuma ba da ita har abada ga zuriyar Ibrahim abokinka?

  13. Ku san cewa Ubangiji ya keɓe masu tsoron Allah wa kansa; Ubangiji zai ji sa’ad da na yi kira gare shi.

  14. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi. Bisa ga sheminit. Zabura ta Dawuda. Ka taimaka, Ubangiji, gama masu tsoron Allah ba sa nan kuma; masu aminci sun ɓace daga cikin mutane.

  15. Game da tsarkakan da suke cikin ƙasar kuwa, su ne masu ɗaukakar da dukan farin cikina ya dangana.

  16. “Ka ji addu’ata, ya Ubangiji, ka saurari kukata ta neman taimako; kada ka kurmance ga kukata. Gama ina zama tare da kai kamar baƙo, baƙo, kamar yadda dukan kakannina sun kasance.

  17. Idanuna za su kasance a kan amintattu a cikin ƙasar, don su zauna tare da ni; tafiyarsa ba ta da zargi zai yi mini hidima.

  18. Ya ku zuriyar Ibrahim bawansa, Ya ku ’ya’yan Yaƙub, zaɓaɓɓensa.

  19. Gama Ubangiji ya zaɓi Yaƙub ya zama nasa, Isra’ila ya zama mallakarsa mai daraja.

  20. Ya tayar wa mutanensa ƙaho, yabon dukan tsarkakansa, na Isra’ila, mutanen da suke kurkusa da zuciyarsa. Yabi Ubangiji.

  21. Bari Isra’ila su yi farin ciki da Mahaliccinsu; bari mutanen Sihiyona su yi murna da Sarkinsu.

  22. kuma fansassu na Ubangiji za su komo. Za su shiga Sihiyona da rerawa; matuƙar farin ciki zai mamaye su. Murna da farin ciki za su sha kansu, baƙin ciki kuma da nishi za su gudu.

  23. Yakan lura da garkensa kamar makiyayi. Yakan tattara tumaki wuri ɗaya yă riƙe su kurkusa da ƙirjinsa; a hankali kuma yakan bi da masu ba da mama.

  24. Kada ku firgita kada kuma ku ji tsoro. Ban furta wannan na kuma yi faɗar haka tuntuni ba? Ku ne shaiduna. Akwai wani Allah in ban da ni? A’a, babu wani Dutse; ban san da wani ba.”

  25. Waɗanda Ubangiji ya fansar za su dawo. Za su shiga Sihiyona da waƙoƙi; madawwamin farin ciki zai rufe kansu da rawani. Murna da farin ciki zai cika su, baƙin ciki da nishi zai ɓace.