Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sieges

134 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yoshuwa kuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Lakish zuwa Eglon; suka yi shiri suka kai mata hari.

  2. A ranan nan suka ci ƙasar da yaƙi, suka buge ta, suka karkashe kowa da takobi kamar dai yadda suka yi a Lakish.

  3. Sai Yoshuwa da dukan Isra’ilawa suka tashi daga Eglon zuwa Hebron suka kai hari a can.

  4. Suka ci birnin da yaƙi, suka karkashe mazaunanta, da sarkin, har da ƙauyukan, ba wanda ya tsira kamar yadda ya yi wa Eglon. Ya hallakar da ita sarai duk da kowane mutum da yake cikinta.

  5. Yoshuwa da Isra’ilawa duka suka juya suka kai wa Debir hari,

  6. suka hallaka birnin, da sarkinta da ƙauyukanta, suka karkashe dukan mazaunan wurin, ba su bar wani da rai ba. Suka yi wa Debir da sarkinta yadda suka yi wa Libna da sarkinta da kuma Hebron.

  7. Saboda haka Abimelek da dukan mutanensa suka tashi da dare suka ɓuya kusa da Shekem a ƙungiyoyi huɗu.

  8. Saboda haka ya ɗauki mutanensa, ya raba su ƙungiya uku, sa’an nan ya yi kwanto a gonakin. Sa’ad da ya ga mutanen suna fitowa daga birni, sai ya yi wuf ya fāɗa musu.

  9. Abimelek da ƙungiyoyin da suke tare da shi suka yi maza suka yi tsaya a ƙofar birnin. Sa’an nan ƙungiyoyi biyu suka ruga suka fāɗa wa waɗanda suke a gonaki suka karkashe su.

  10. Dukan yinin, Abimelek ya matsa yaƙi da birnin sai da ya cinye ta ya kuma kashe mutanenta. Sa’an nan ya hallaka birnin ya barbaza gishiri a kanta.

  11. Biye da wannan Abimelek ya tafi Tebez, ya kewaye ta ya kuma cinye ta da yaƙi.

  12. Nahash mutumin Ammon ya haura ya kewaye Yabesh Gileyad da yaƙi. Dukan mutanen Yabesh suka ce masa, “Ka ƙulla amana da mu, mu kuwa za mu bauta maka.”

  13. Amma Nahash ya ce, “Zan ƙulla amana da ku kawai a kan sharaɗin cewa zan ƙwaƙulo idon dama na kowannenku, ta haka za a kunyata Isra’ila.”

  14. Dattawan Yabesh suka ce masa, “Ka ba mu kwana bakwai don mu aika manzanni a dukan ƙasar Isra’ila idan ba mu sami wanda zai cece mu ba, za mu ba da kanmu gare ka.”

  15. Gari yana wayewa, sai Shawulu ya raba mutane kashi uku, a sa’a ta ƙarshe na daren sai suka fāɗa wa sansanin Ammonawa, suka kuma karkashe su har lokacin da rana ta yi zafi. Waɗanda suka kuɓuce kuwa suka warwatsu, har babu biyunsu da aka bari tare.

  16. Sa’ad da aka ce wa Dawuda, “Duba ga Filistiyawa suna yaƙi da mutanen Keyila, suna kwashe musu hatsi a masussukai.”

  17. Sa’an nan Dawuda da mutanensa suka tafi Keyila, suka yi yaƙi da Filistiyawa, suka kwashe musu shanunsu, suka jijji wa Filistiyawa ƙwarai, suka cece mutanen Keyila daga hannunsu.

  18. A rana ta uku, Dawuda da mutanensa suka isa Ziklag, sai suka tarar Amalekawa sun riga sun kawo wa Negeb da Ziklag hari. Suka cinye Ziklag, suka ƙone ta,

  19. suka kwashe mata, yara da tsofaffi da dukan abubuwan da suke cikin garin. Ba su kashe kowa ba, amma suka kwashe su, suka tafi.

  20. Da bazara, a lokacin da sarakuna sukan fita zuwa yaƙi, sai Dawuda ya aiki Yowab tare da mutanen sarki, da dukan Isra’ila. Suka je suka hallaka Ammonawa, suka kuma yi wa Rabba kwanton ɓauna. Amma Dawuda ya yi zamansa a Urushalima.

  21. wataƙila sarki yă husata, yă tambaye ka, ‘Me ya sa kuka je kusa da birnin don ku yi yaƙi? Ba ku san cewa za su yi harbi daga katanga ba?

  22. Wane ne ya kashe Abimelek ɗan Yerub-Beshet? Ba mace ce ta jefa dutsen niƙa a kansa daga katanga, ta haka ya mutu a Tebez ba? Me ya sa kuka je kurkusa da katangar?’ In ya tambaye ka wannan, sai ka ce masa, ‘Har bawanka Uriya mutumin Hitti ma ya mutu.’ ”

  23. Ana cikin haka, sai Yowab ya yi yaƙi da Rabba na Ammonawa, ya kuma ƙwace babban birnin.

  24. Sa’an nan Yowab ya aika manzanni wurin Dawuda yana cewa, “Na yaƙi Rabba na kuma ƙwace hanyar samun ruwanta.

  25. Yanzu fa ka tattara saura rundunoni ka fāɗa wa birnin ka ci shi. In ba haka ba zan karɓe birnin, a kuma kira shi da sunana.”