Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sieges

134 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Haka birnin ta kasance a kewaye har shekara ta goma sha ɗaya ta mulkin Zedekiya.

  2. A rana ta tara ta watan huɗu, lokacin da yunwa ta yi tsanani a birnin, babu kuma abinci domin mutane su ci.

  3. Bayan dukan abin da Hezekiya ya yi cikin aminci, sai Sennakerib sarkin Assuriya ya zo ya yaƙi Yahuda. Ya yi kwanto wa biranen katanga, yana zato zai ci su da yaƙi wa kansa.

  4. sai ya yi shawara da fadawansa da hafsoshin mayaƙansa cewa su datse ruwa daga maɓulɓulan ruwan da yake waje da birnin, suka kuwa taimake shi.

  5. Sai babban taro suka haɗu suka datse dukan maɓulɓulai da rafuffukan da suke gudu cikin ƙasar. Suka ce “Me zai sa sarakunan Assuriya su zo su sami ruwa barkatai?”

  6. Sai suka yi aiki tuƙuru suna gyaran dukan sassan katangar da suka fāɗi, suna kuma gina hasumiya a kai. Ya gina wata katanga a waje da wannan, ya kuma ƙara ƙarfin madogaran gini na Birnin Dawuda. Ya yi makamai masu yawa da kuma garkuwoyi.

  7. Ya naɗa manyan hafsoshi a kan mutane, ya tattara su a gabansa a fili a ƙofar birni, ya kuma ƙarfafa su da waɗannan kalmomi.

  8. “Ku ƙarfafa, ku yi ƙarfin hali. Kada ku ji tsoro ko ku yi fargaba saboda sarkin Assuriya, da mayaƙan nan masu yawa da suke tare da shi, gama shi wanda yake tare da mu, ya fi wanda yake tare da su.

  9. Mayaƙa na jiki ne kawai suke tare da shi, amma Ubangiji Allahnmu ne yake tare da mu, zai kuwa taimake mu yă kuma yi yaƙinmu.” Mutane kuwa suka amince da maganar Hezekiya, Sarkin Yahuda.

  10. Sa’an nan suka yi magana da ƙarfi cikin Yahudanci wa mutanen Urushalima waɗanda suke kan katanga, don su firgita su, su kuma sa su ji tsoro don su iya cin birnin.

  11. Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.

  12. Ɗan’uwan da aka yi wa laifi ya fi birni mai katanga wuyan shiryawa, kuma faɗace-faɗace suna kama da ƙofofin ƙarfe na fada.

  13. An bar diyar Sihiyona kamar rumfar mai ƙumu a gonar inabi, kamar bukka a gonar kabewa, kamar birnin da aka kewaye da yaƙi.

  14. kuka ga cewa Birnin Dawuda tana da wuraren kāriya masu yawa da suka tsattsage; kuka tattara ruwa a Tafkin Ƙasa.

  15. Kuka ƙirga gine-gine a Urushalima kuka kuma rurrushe gidaje don ku ƙarfafa katanga.

  16. Zan kashe waɗanda suke zaune a wannan birni, mutane da dabbobi za su kuwa mutu da muguwar annoba.

  17. “Duba yadda aka gina mahaurai don a kame birni. Saboda takobi, yunwa da annoba, za a ba da birnin ga Babiloniyawa waɗanda suka kewaye shi da yaƙi. Abin da ka faɗa ya faru, yadda kake gani yanzu.

  18. Gama zan kuta in kuma kawo a kan Babilon haɗinkan manyan al’ummai na arewa. Za su ja dāgār gāba da ita, kuma daga arewa za a ci ta da yaƙi. Kibiyoyinsu za su zama kamar na gwanayen jarumawa waɗanda ba sa dawowa hannu wofi.

  19. Ku zo ku yi gāba da ita daga nesa. Ku buɗe rumbunanta; ku jibga ta kamar tsibin hatsi. Ku hallaka ta sarai kada ku bar mata raguwa.

  20. Ku kashe dukan ’yan bijimanta bari su gangara zuwa mayanka! Kaitonsu! Gama ranansu ta zo, lokaci ya yi da za a hukunta su.

  21. Saboda haka, samarinta za su fāɗi a tituna; za a kawar da dukan sojojinta a wannan rana,” in ji Ubangiji.

  22. Zan aika da baƙi zuwa Babilon su casa ta su kuma yi kaca-kaca da ƙasarta; za su yi hamayya da ita a kowane gefe a ranar masifarta.

  23. Ku tā da tuta gāba da katangan Babilon! Ku ƙara matsara, ku kafa masu tsaro, ku shirya kwanto! Ga shi, Ubangiji zai aikata abin da ya faɗa umarninsa a kan mutanen Babilon.

  24. Sa’an nan ka yi mata ƙawanya. Ka kafa mata katangar ƙawanya, ka gina katangar da ɗan tudu ka kewaye ta da dundurusai.

  25. Wanda yake da nisa zai mutu da annoba, shi da yake kusa kuma zai mutu ta takobi, wanda kuma ya tsira aka kuma bari zai mutu da yunwa. Ta haka zan aukar da fushina a kansu.