Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Sieges

134 ayoyi · 63 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Dawuda ya tattara sauran rundunar sojojin suka tafi Rabba suka fāɗa masa suka kuma ci shi.

  2. A shekara ta ashirin da bakwai na Asa sarkin Yahuda, Zimri ya yi mulki a Tirza kwana bakwai. Mayaƙa suka yi sansani kusa da Gibbeton, wani garin Filistiyawa.

  3. Sai Omri da dukan Isra’ilawa suka janye daga Gibbeton, suka yi wa Tirza kwanto.

  4. Ben-Hadad sarkin Aram kuwa ya tattara mayaƙansa gaba ɗaya. Sarakuna talatin da biyu suka tafi tare da shi haɗe da dawakansu da kekunan yaƙinsu. Ya haura ya yi wa Samariya kwanto, ya kuma yaƙe ta.

  5. Ya aika da ’yan aika zuwa cikin birnin wurin Ahab sarkin Isra’ila yana cewa, “Ga abin da Ben-Hadad ya ce,

  6. ‘Azurfarka da zinariyarka nawa ne. Mafi kyau cikin matanka da ’ya’yanka nawa ne.’ ”

  7. Saboda haka ya tambayi Yehoshafat, ya ce, “Za ka tafi tare da ni don in yi yaƙi da Ramot Gileyad?” Yehoshafat ya amsa wa sarkin Isra’ila, ya ce, “Ni ma kamar ka ne, mutanena kuwa kamar mutanenka, dawakaina kamar dawakanka.”

  8. Sai sarkin Isra’ila da Yehoshafat sarkin Yahuda suka haura zuwa Ramot Gileyad.

  9. Sai ya aika da dawakai da kekunan yaƙi da babban rukunin soja zuwa can. Suka bi dare, suka kewaye birnin.

  10. Bayan wani lokaci, Ben-Hadad sarkin Aram ya tattara dukan rundunarsa, ya je ya kewaye Samariya da yaƙi.

  11. Yayinda sarkin Isra’ila yake wucewa kusa da katanga, sai wata mace ta yi masa kuka ta ce, “Ka taimake ni, ranka yă daɗe, sarki!”

  12. Sai sarki ya amsa ya ce, “In Ubangiji bai taimake ki ba, me zan iya yi? Ina da hatsi ko ruwan inabin da zan ba ki ne?”

  13. Sa’an nan ya tambaye ta ya ce, “Me ya faru?” Sai ta amsa ta ce, “Wannan mace ta ce mini, ‘Kawo ɗanki mu ci yau, gobe kuwa mu ci ɗana.’

  14. Saboda haka muka dafa ɗana muka ci. Kashegari na ce mata, ‘Kawo ɗanki mu ci,’ amma ta ɓoye shi.”

  15. A zamanin Feka sarkin Isra’ila, Tiglat-Fileser sarkin Assuriya ya zo ya kama Iyon, Abel-Bet-Ma’aka, Yanowa da Kedesh da kuma Hazor. Ya kame Gileyad da Galili, haɗe da dukan ƙasar Naftali, ya kuma kwashi mutanen zuwa Assuriya.

  16. Sarkin Assuriya ya kai wa ƙasar Hosheya gaba ɗaya farmaki, ya kewaye Samariya na tsawon shekara uku.

  17. A shekara ta goma sha huɗu ta mulkin sarkin Hezekiya, sai sarki Sennakerib sarkin Assuriya ya kai farmaki wa biranen Yahuda masu katanga ya kuma kama su.

  18. Suka kira sarki, sai Eliyakim ɗan Hilkiya sarkin fada, da Shebna magatakarda, da Yowa ɗan Asaf marubuci suka je wurinsu.

  19. Ka ce kana da dabara da ƙarfin soji, amma bagu kawai kake yi. Da wa ka dogara har da za ka yi mini tawaye?

  20. Sai Eliyakim ɗan Hilkiya, da Shebna, da Yowa suka ce wa jagoran dakarun, “Muna roƙonka ka yi wa bayinka magana da harshen Arameyik da yake muna ji. Kada ka yi mana magana da Yahudanci domin kada mutanen da suke bisa katanga su ji!”

  21. Na tona rijiyoyi a ƙasashen waje na kuma sha ruwa a can. Da tafin ƙafafuna na busar da dukan rafuffukan Masar.”

  22. “Saboda haka ga abin da Ubangiji ya ce game da sarkin Assuriya, “Ba zai shiga birnin nan ba ko yă harba kibiya a nan. Ba zai kusace ta da garkuwa ko yă yi mata zoben yaƙi ba.

  23. A wannan lokaci, hafsoshin Nebukadnezzar sarkin Babilon suka kawo wa Urushalima yaƙi, suka kuma kewaye ta.

  24. Nebukadnezzar na Babilon da kansa kuwa ya zo birnin yayinda hafsoshinsa suka kewaye ta.

  25. A rana ta goma ga wata na goma, a shekara ta tara ta mulkin Zedekiya ne Nebukadnezzar sarkin Babilon tare da dukan rundunan yaƙinsa, ya tasam wa Urushalima. Ya yi sansani a bayan birnin, ya kewaye ta da shirin yaƙi.