Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reproof

165 ayoyi · 70 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Da kayan kiɗi masu tsirkiya. Bisa ga sheminit. Ta Dawuda. Ya Ubangiji, kada ka tsawata mini cikin fushinka ko ka hore ni cikin hasalarka.

  2. Dokar Ubangiji cikakkiya ce, takan wartsakar da rai. Farillan Ubangiji abin dogara ne, suna mai da hikima da sauƙi.

  3. Ƙa’idodin Ubangiji daidai ne, suna ba da farin ciki ga zuciya. Umarnan Ubangiji haske ne suna ba da haske ga idanu.

  4. Tsoron Ubangiji yakan kawo tsabtar zuciya, zai kasance har abada. Farillan Ubangiji tabbatattu ne, kuma gaba ɗaya masu adalci ne.

  5. Sun fi zinariya daraja, fiye da zalla zinariya nesa; sun fi zuma zaƙi fiye da zuma daga kaki.

  6. Ta wurinsu ana gargaɗe bawanka; a kiyaye su akwai lada mai girma.

  7. Kakan tsawata ka kuma hore mutane saboda zunubinsu; kakan cinye wadatarsu kamar yadda asu ke yi, kowane mutum dai shaƙar iska ne. Sela

  8. Kun yi waɗannan abubuwa na kuwa yi shiru; kun ɗauka gaba ɗaya ni kamar ku ne. Amma zan tsawata muku in kuma zarge ku a fuskarku.

  9. Mai albarka ne mutumin da ka yi masa horo, ya Ubangiji, mutumin da ka koyar daga dokarka;

  10. Kafin in sha wahala na kauce, amma yanzu ina biyayya da maganarka.

  11. Ya yi kyau da na sha wahala don in koyi ƙa’idodinka.

  12. Ya Ubangiji na sani, cewa dokokinka masu adalci ne, kuma cikin aminci ka hore ni.

  13. Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.

  14. da yake ba su karɓi shawarata ba suka kuwa yi kunnen ƙashi ga tsawatata,

  15. Za ku ce, “Me ya sa na ƙi horo! Me ya sa zuciyata ta ƙi gyara!

  16. Gama waɗannan umarnai fitila ne, wannan koyarwa haske ne, kuma gyare-gyaren horo hanyar rayuwa ce,

  17. “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.

  18. Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.

  19. Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.

  20. Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.

  21. Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.

  22. Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.

  23. Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu.

  24. Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba.

  25. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.