Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reproof: General references

41 ayoyi · 70 fannoni

Ayoyi game da General references

Tace bisa littafi
  1. “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

  2. Bari mutum mai adalci yă buge ni, alheri ne; bar shi yă tsawata mini, mai ne a kaina. Kaina ba zai ƙi shi ba, duk da haka addu’ata kullum tana gāba da mugayen ayyuka.

  3. “Duk wanda ya yi wa mai ba’a gyara yana gayyatar zagi duk wanda ya tsawata wa mugu yakan gamu da cin mutunci.

  4. Kada ka tsawata wa masu ba’a gama za su ƙi ka; ka tsawata wa mai hikima zai kuwa ƙaunace ka.

  5. Duk wanda ya mai da hankali ga horo kan nuna hanyar rai, amma duk wanda ya ƙyale gyara kan sa waɗansu su kauce.

  6. Duk mai ƙaunar horo yana ƙaunar sani, amma duk mai ƙin gyara wawa ne.

  7. Duk wanda ya ƙyale horo yakan kai ga talauci da kuma kunya, amma duk wanda ya karɓi gyara yakan sami girma.

  8. Wawa yakan ƙi kulawa da horon da mahaifinsa yake masa, amma duk wanda ya yarda da gyara kan nuna azanci.

  9. Horo mai tsanani yana jiran duk wanda ya bar hanya; wanda ya ƙi gyara zai mutu.

  10. Mai yin ba’a yakan ƙi gyara; ba zai nemi shawara mai hikima ba.

  11. Duk wanda ya mai da hankali sa’ad da ake tsawata masa ba zai kasance dabam a cikin masu hikima ba.

  12. Duk waɗanda suka ƙi horon sun rena kansu ke nan, amma duk waɗanda sun yarda da gyara sukan ƙara basira.

  13. Tsawata kan sa mutum ya koyi basira fiye da abin da wawa zai koya ko da an dūke shi sau ɗari.

  14. Ka bulale mai ba’a, marasa azanci kuwa za su yi la’akari; ka tsawata wa mai basira, zai kuwa ƙara sani.

  15. Sa’ad da aka hukunta mai ba’a marasa azanci suka yi wayo; sa’ad da aka yi wa mai hikima umarni yakan sami sani.

  16. Kamar ’yan kunnen zinariya ko kuwa kayan ado na zinariya zalla haka yake da tsawatawar mai hikima ga kunne mai saurarawa.

  17. Ka amsa wa wawa bisa ga wautarsa, in ba haka ba zai ga kansa mai hikima ne.

  18. Gara tsawatawar da ake yi a fili da ƙaunar da ake yi a ɓoye.

  19. Za a iya amince da rauni daga aboki, amma abokin gāba ko da ya sumbace ka kada ka sake da shi!

  20. Duk wanda ya tsawata wa wani mutum zai sami yabo a ƙarshe fiye da wanda yake mai daɗin baki.

  21. Gara ka saurari tsawatawar mai hikima da ka saurari waƙar wawaye.

  22. Ba ku son mai yin gaskiya a ɗakin shari’a kuna ƙin mai faɗar gaskiya.

  23. “In ɗan’uwanka ya yi maka laifi, ka je ka nuna masa laifinsa, tsakaninku biyu kaɗai. In ya saurare ka, ka maido da ɗan’uwanka ke nan.

  24. Amma in bai saurare ka ba, ka je tare da mutum ɗaya ko biyu, domin ‘a tabbatar da kowace magana a bakin shaidu biyu ko uku.’

  25. In kuwa ya ƙi yă saurare su, sai ka gaya wa ikkilisiya; in kuma ya ƙi yă saurari ikkilisiya ma, ka yi da shi kamar marar sanin Allah ko mai karɓar haraji.