Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reproof: Of those who offend, a warning to others

7 ayoyi · 70 fannoni

Ayoyi game da Of those who offend, a warning to others

  1. “ ‘Kada ka yi ƙiyayyar ɗan’uwanka a zuciya. Ka tsawata wa maƙwabcinka da gaske don kada ka sami rabo cikin laifinsa.

  2. Sai Bitrus ya ce, “Ananiyas, ta yaya Shaiɗan ya cika zuciyarka haka da ka yi wa Ruhu Mai Tsarki ƙarya ka kuma ajiye wa kanka sauran kuɗin da ka karɓa na filin?

  3. Ba naka ba ne kafin ka sayar da shi? Bayan da ka sayar da shi kuma, kuɗin ba naka ba ne? Me ya sa ka yi tunanin yin irin wannan abu? Ba mutum ne ka yi wa ƙarya ba, Allah ne ka yi masa.”

  4. Bitrus ya ce mata, “Ta yaya kuka yarda ku gwada Ruhun Ubangiji? Duba! Sawun mutanen da suka binne mijinki suna bakin ƙofa, za su kuwa ɗauke ki zuwa waje ke ma.”

  5. Amman waɗannan dattawa waɗanda suke yin zunubi kuwa sai ka kwaɓe su a gaban jama’a, don saura su ji tsoro.

  6. Gama akwai ’yan tawaye da yawa, masu surutun banza da masu ruɗi, musamman ƙungiyar masu kaciya.

  7. Wannan shaida gaskiya ce. Saboda haka, sai ka tsawata musu sosai, don su zama sahihai a wajen bangaskiya,