Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophecy

120 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sojojin nan matasa na shugabannin yankuna suka taka suka fita daga birnin da mayaƙa a bayansu.

  2. Kowannensu kuwa ya buge abokin gābansa. Ganin wannan, sai Arameyawa suka gudu, Isra’ilawa suna bi. Amma Ben-Hadad na Aram ya tsere a kan dokinsa tare da waɗansu mahayan dawakansa.

  3. Sarki Isra’ila ya bi, ya kuma sha ƙarfin dawakan da keken yaƙin, ya kashe Arameyawa da yawa.

  4. Daga baya, annabin ya zo wurin sarkin Isra’ila ya ce, “Ka ƙarfafa matsayinka ka kuma ga abin da za a yi, gama a bazara mai zuwa sarkin Aram zai sāke kawo yaƙi.”

  5. Ana cikin haka, shugabannin sarkin Aram suka ba shi shawara, “Allolinsu, allolin tuddai ne. Shi ya sa suka fi mu ƙarfi. Amma in mun yaƙe su a fili, tabbatacce za mu fi su ƙarfi.

  6. Ka yi wannan. Ka cire dukan sarakuna daga matsayinsu ka sa waɗansu shugabanni a maimakonsu.

  7. Dole kuma ka tā da waɗansu mayaƙa kamar waɗanda ka rasa, doki don doki, keken yaƙi kuma don keken yaƙi, saboda mu iya yaƙe Isra’ila a fili. Ta haka tabbatacce za mu fi ƙarfinsu.” Sai ya yarda da su, ya kuma yi haka.

  8. Bazara na biye Ben-Hadad ya tattara Arameyawa, ya haura zuwa Afek don yă yaƙi Isra’ila.

  9. Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.

  10. Sai mutumin Allah ya zo ya ce wa sarkin Isra’ila, “Ga abin da Ubangiji ya ce, ‘Domin Arameyawa suna tsammani Ubangiji allahn tuddai ne, ba allahn kwari ba, zan ba da wannan ɗumbun mayaƙa a hannuwanka, za ka kuwa sani ni ne Ubangiji.’ ”

  11. Kwana bakwai suka yi sansani ɗaura da juna, a rana ta bakwai sai yaƙi ya haɗu. Isra’ilawa suka kashe sojojin kafa na Arameyawa dubu ɗari a rana ɗaya.

  12. Sauransu suka tsere zuwa birnin Afek, inda katangar ya fāɗa a kan mutum dubu ashirin da bakwai. Sai Ben-Hadad ya gudu zuwa birni ya ɓuya a ciki cikin ɗaki.

  13. Da sassafe suka tashi suka nufi Hamadan Tekowa. Yayinda suka kama hanya, Yehoshafat ya tsaya ya ce, “Ku saurare ni, Yahuda da mutanen Urushalima! Ku amince da Ubangiji Allahnku za a kuwa kafa ku; ku amince da annabawansa za ku kuwa yi nasara.”

  14. Sauran ayyukan mulkin Manasse, haɗe da addu’arsa ga Allahnsa da kuma kalmomin da mai duba ya yi masa cikin sunan Ubangiji, Allah na Isra’ila, suna a rubuce cikin tarihin sarakunan Isra’ila.

  15. Sai Ubangiji Allah na kakanninsu, ya yi ta aika da magana gare su ta wurin ’yan saƙonsa sau da sau, domin ya ji tausayi mutanensa da mazauninsa.

  16. Shekaru masu yawa ka yi haƙuri da su. Ta wurin Ruhunka ka gargaɗe su ta wurin annabawa. Duk da haka ba su kasa kunne ba, saboda haka ka miƙa su ga maƙwabtansu.

  17. Yanzu ku daina ba’arku, in ba haka ba sarƙoƙinku za su ƙara nauyi; Ubangiji, Ubangiji Maɗaukaki, ya faɗa mini game da hallakar da aka ƙaddara a kan dukan ƙasar.

  18. Dukan al’ummai su taru mutane kuma su tattaru. Wane ne a cikinsu ya yi faɗar wannan ya kuma yi mana shelar abubuwan da suka riga suka faru? Bari su kawo shaidunsu don su tabbatar cewa sun yi daidai, don waɗansu su ji su kuma ce, “Gaskiya ne.”

  19. Wane ne kuwa kama da ni? Ya faɗa a ji. Bari yă yi shela ya kuma nuna shi a gabana mene ne ya faru tun da na kafa mutanena na dā, mene ne kuma bai riga ya faru ba, I, bari yă faɗa abin da zai zo.

  20. wanda ya tabbatar da maganganun bayinsa ya kuma cika annabce-annabcen ’yan aikansa, “wanda ya ce game da Urushalima, ‘Za a zauna a cikinta,’ game da garuruwan Yahuda, ‘Za a gina su,’

  21. Furta abin da zai kasance, ku gabatar da shi, bari su yi shawara tare. Wa ya faɗa wannan tuntuni, wa ya yi shelar sa a kwanakin dā? Ba ni ba ne, Ubangiji? Kuma babu Allah in ban da ni, Allah mai adalci da kuma Mai Ceto; babu wani sai ni.

  22. “Kafin in siffanta ka a cikin ciki na san ka, kafin a haife ka, na keɓe ka; na naɗa ka ka zama annabi ga al’ummai.”

  23. Daga lokacin da kakanninku suka bar Masar har yă zuwa yau, kullum na yi ta aikan bayina annabawa.

  24. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ka yi shelar dukan maganan nan a biranen Yahuda da titunan Urushalima duka cewa, ‘Su saurari zancen alkawarin nan, su aikata.

  25. Sai Ubangiji ya ce mini, “Annabawa suna ta annabcin ƙarya da sunana. Ban aike su ba, ban kuma naɗa su ba, ban yi musu magana ba. Suna muku annabci wahayin ƙarya, suna muku duba marar amfani, suna bautar gumaka suna kuma bayyana tunanin kansu ne.