Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prophecy

120 ayoyi · 47 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Kada ku rena annabci,

  2. Dukan Nassi numfashin Allah ne yana kuma da amfani don koyarwa, tsawatarwa, gyara da kuma horarwa cikin adalci,

  3. ’Yan’uwa, ku ɗauki annabawa da suka yi magana a cikin sunan Ubangiji, a matsayin gurbi na haƙuri a cikin shan wahala.

  4. Game da ceton nan, annabawa, waɗanda suka yi maganar alherin da za tă zo gare ku, sun yi bincike mai zurfi, a natse,

  5. suna ƙoƙari su san lokaci da kuma yanayin da Ruhun Kiristi da yake cikinsu yana nunawa sa’ad da ya yi faɗi a kan wahalolin Kiristi da kuma ɗaukaka da za tă bi.

  6. Aka bayyana musu cewa ba kansu ne suke bauta wa ba sai ku, sa’ad da suka yi maganar abubuwan da aka faɗa muku ta wurin waɗanda suka yi muku wa’azin bishara, ta wurin Ruhu Mai Tsarki wanda aka aika daga sama. Ko mala’iku ma suna marmari su ga waɗannan abubuwa.

  7. Muna kuwa da maganar annabawa da aka ƙara tabbatar mana, zai fi kyau in kuka lura da ita, kamar hasken da yake haskakawa a wuri mai duhu, har yă zuwa wayewar gari da kuma haskakawar tauraron asubahi a zukatanku.

  8. Gaba da kome dai, dole ku gane cewa babu annabcin Nassin da ya fito daga fassarar annabi da kansa.

  9. Gama annabci bai taɓa samo tushensa daga nufin mutum ba, sai dai mutane sun yi magana daga Allah yayinda Ruhu Mai Tsarki ya bishe su.

  10. Cikin kwaɗayinsu waɗannan malaman ƙarya za su cuce ku da tatsuniyoyin da suka ƙaga. Hukuncinsu yana a rataye a kansu tun da daɗewa, hallakarsu kuma ba ta barci.

  11. ’Ya’yana ƙaunatattu, waɗannan su ne kwanakin ƙarshe; kuma kamar yadda kuka ji cewa magabcin Kiristi yana zuwa, ko yanzu ma abokan gāban Kiristi da yawa sun zo. Ta haka muka san cewa kwanakin ƙarshe sun iso.

  12. Amma ku abokaina ƙaunatattu, ku tuna da abin da manzannin Ubangijinmu Yesu Kiristi suka faɗa a dā.

  13. Sun ce muku, “A kwanakin ƙarshe za a kasance da masu ba’a waɗanda za su bi sha’awace-sha’awacensu na rashin tsoron Allah.”

  14. Wahayin Yesu Kiristi, wanda Allah ya ba shi yă nuna wa bayinsa abin da lalle zai faru nan ba da daɗewa ba. Ya bayyana shi ta wurin aiko da mala’ikansa zuwa ga bawansa Yohanna,

  15. Mai albarka ne wanda yake karanta waɗannan kalmomin annabci, masu albarka ne kuma waɗanda suke jinsu, suke kuma sa abin da aka rubuta a ciki a zuciya, domin lokaci ya yi kusa.

  16. Kada ka ji tsoron wahalar da kake gab da sha. Ina gaya maka, Iblis zai sa waɗansunku a kurkuku don yă gwada ku. Za ku sha tsanani na kwana goma. Ka yi aminci ko da za a kashe ka, ni kuwa zan ba ka rawanin rai.

  17. Zan kuma ba wa shaiduna nan biyu iko, za su kuwa yi annabci na kwanaki 1,260, saye da gwadon makoki.”

  18. “Ga shi! Ina zuwa da wuri! Mai albarka ne wanda yake kiyaye kalmomin annabcin da suke cikin wannan littafi.”

  19. Ina yin wa duk wanda ya ji kalmomin annabcin wannan littafi gargaɗi. Duk wanda ya ƙara wani abu a kansu, Allah zai ƙara masa annoban da aka bayyana a littafin nan.

  20. Duk wanda kuma ya yi ragi a kalmomi daga littafin annabcin nan, Allah zai ɗauke rabonsa na itacen rai da kuma na birnin nan mai tsarki, waɗanda aka bayyana a littafin nan.