Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins

152 ayoyi · 34 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku ɗauki magana tare da ku ku komo wurin Ubangiji. Ku ce masa, “Ka gafarta mana dukan zunubanmu ka kuma karɓe mu da alheri, don mu iya yabe ka da leɓunanmu.

  2. “Ko yanzu”, in ji Ubangiji, “Ku juyo gare ni da dukan zuciyarku, da azumi da kuka da makoki.”

  3. Bari firistocin da suke yin hidima a gaban Ubangiji, su yi kuka tsakanin filin haikali da bagade. Bari su ce, “Ka cece mutanenka, ya Ubangiji. Kada ka bar gādonka yă zama abin dariya, da abin ba’a a cikin al’ummai. Me zai sa a ce a cikin mutane, ‘Ina Allahnsu yake?’ ”

  4. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Yahuda, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Gama sun ƙi bin dokar Ubangiji ba su kuma yi biyayya da ƙa’idodinsa ba, domin allolin ƙarya sun ruɗe su, allolin da kakanninsu suka bauta.

  5. Ku ji wannan maganar da Ubangiji ya yi game da ku, ya ku jama’ar Isra’ila, a kan dukan iyalin da na fitar daga Masar.

  6. “Ku ne kaɗai na zaɓa cikin dukan al’umman duniya; saboda haka zan hukunta ku saboda dukan zunubanku.”

  7. “Na ƙi, ina kuma ƙyamar bukukkuwanku na addini; ba na son ganin tarurrukanku.

  8. Ko da kun kawo mini hadayu na ƙonawa da kuma hadayu na hatsi, ba zan karɓa ba. Ko da kun kawo zaɓaɓɓun hadayu na zumunta, ba zan ɗauke su a bakin kome ba.

  9. “Ranakun suna zuwa,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka, “sa’ad da zan aika da yunwa cikin ƙasar, ba yunwar abinci ko ta ƙishirwa ba, sai dai yunwa ta jin maganar Ubangiji.

  10. “Tafi babban birnin nan Ninebe ka yi mata wa’azi, saboda muguntarta ta haura zuwa gabana.”

  11. Mutanen Ninebe kuwa suka gaskata Allah. Aka yi shela a yi azumi, sai dukansu daga babba har zuwa ƙaraminsu, suka sa tufafin makoki.

  12. Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.

  13. Ku tafi, ku ba ni wuri! Gama wannan ba wurin hutunku ba ne, gama ya ƙazantu, ya zama kangon da ya wuce gyara.

  14. Kaiton birni mai zub da jini, wadda take cike da ƙarairayi, cike da ganima, wadda ba a rasa masu fāɗawa cikin wahala!

  15. Sai annabi Haggai ya ce, “ ‘Haka yake da wannan mutane da kuma wannan al’umma a gabana,’ in ji Ubangiji. ‘Duk abin da suke yi da kuma dukan abin da suke miƙawa ƙazantattu ne.

  16. “Kaitonki, Korazin! Kaitonki, Betsaida! Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne aka yi a Taya da Sidon, da tuni sun tuba sanye da rigar makoki da toka.

  17. Amma ina gaya muku, za a fi jin tausayin Taya da Sidon a ranar shari’a, fiye da ku.

  18. Ke kuma Kafarnahum, za a ɗaga ki sama ne? A’a, za ki gangara zuwa zurfafa ne. Da a ce ayyukan banmamakin da aka yi a cikinki ne a aka yi a Sodom, da tana nan har yă zuwa yau.

  19. Amma ina gaya miki, za a fi jin tausayin Sodom fiye da ke a ranar shari’a.”

  20. Ta haka alhakin jinin masu adalcin da aka zubar a duniya, tun daga jinin Habila mai adalci, zuwa jinin Zakariya ɗan Berekiya, wanda kuka kashe tsakanin haikali da bagade zai koma kanku.

  21. Gaskiya nake gaya muku, duk wannan zai auko wa wannan zamani.

  22. “Urushalima, ayya Urushalima, ke da kike kashe annabawa, kike kuma jifan waɗanda aka aiko gare ki, sau da sau na so in tattara ’ya’yanki wuri ɗaya, yadda kaza takan tattara ’ya’yanta cikin fikafikanta, amma kuka ƙi.

  23. Ga shi, an bar muku gidanku a yashe.

  24. Gama ina gaya muku, ba za ku sāke ganina ba sai kun ce, ‘Mai albarka ne wanda yake zuwa cikin sunan Ubangiji.’ ”

  25. Sai dukan mutane suka amsa, suka ce, “Bari alhakin jininsa yă zauna a kanmu da ’ya’yanmu!”