Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins: Confessed

5 ayoyi · 34 fannoni

Ayoyi game da Confessed

  1. “ ‘Amma in suka tuba daga zunubansu da zunuban kakanninsu, da cin amanar da suka yi mini, da kuma adawar da suka yi da ni,

  2. sa’ad da kuma ku da ’ya’yanku kuka komo ga Ubangiji Allahnku, kuka kuma yi biyayya da dukan zuciyarku da kuma dukan ranku, bisa ga kome da na umarce ku a yau,

  3. Sa’an nan Isra’ilawa suka yi kuka ga Ubangiji, suka ce, “Mun yi maka zunubi, mun bar Allahnmu muka shiga bautar Ba’al.”

  4. in suka canja zuciyarsu a ƙasar da aka riƙe su kamammu, suka tuba, suka kuma roƙe ka a ƙasar waɗanda suka ci su da yaƙi, suka ce, ‘Mun yi zunubi, mun yi abin da ba daidai ba, mun yi mugunta’;

  5. in sun juye gare ka da dukan zuciyarsu, da dukan ransu a ƙasar abokan gābansu waɗanda suka kwashe kamammu, suka yi addu’a gare ka, suka fuskanci wajen ƙasar da ka ba wa kakanninsu, waje birnin da ka zaɓa, da kuma haikalin da na gina domin Sunanka;