Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins: Babylon
Ayoyi game da Babylon
“Ku gudu daga cikin Babilon! Bari kowa yă ceci ransa! Kada a hallaka saboda zunubanta. Gama lokaci ne don ramuwar Ubangiji, zai sāka mata bisa ga alhakinta.
Ke da kike zama kusa da ruwaye da kike kuma wadatar dukiya, ƙarshenki ya zo, lokaci ya yi da za a kau da ke.
“Amma kwanaki suna zuwa,” in ji Ubangiji, “sa’ad da zan hukunta gumakanta, da kuma a dukan ƙasarta waɗanda aka yi wa rauni, za su yi nishi.