Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins: Punishment for

7 ayoyi · 34 fannoni

Ayoyi game da Punishment for

  1. Urushalima tana tangaɗi, Yahuda yana fāɗuwa; maganganunsu da ayyukansu suna gāba da Ubangiji, suna rena ɗaukakar kasancewarsa.

  2. Amma duk al’ummar da ba tă saurara ba, zan tumɓuke ta ɗungum in kuma hallaka ta,” in ji Ubangiji.

  3. “Amma sa’ad da shekaru saba’in ɗin suka cika, zan hukunta sarkin Babilon da kuma al’ummarsa, ƙasar Babiloniyawa, saboda laifinsu,” in ji Ubangiji, “in kuma mai da ita kango har abada.

  4. zan kawo baƙi a kanka, waɗanda suka fi mugunta cikin sauran al’ummai; za su zāre takubansu a kan kyakkyawar hikimarka su kuma ɓarke darajarka mai walƙiya.

  5. Za su jefar da kai cikin rami, za ka kuwa yi muguwar mutuwa a tsakiyar tekuna.

  6. Za ka iya ce yanzu, “Ni allah ne,” a gaban waɗanda suka kashe ka? Za ka zama mutum kurum, ba allah ba, a hannuwan waɗanda suka kashe ka.

  7. Za ka yi mutuwar marar kaciya a hannuwan baƙi. Na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”