Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins: Punishment for, averted on repentance

9 ayoyi · 34 fannoni

Ayoyi game da Punishment for, averted on repentance

  1. Amma Isra’ilawa suka ce wa Ubangiji, “Mu dai mun yi zunubi. Ka yi da mu abin da ka ga dama, amma muna roƙonka ka cece mu a yanzu.”

  2. Sa’an nan suka zubar da allolin nan daga cikinsu suka bauta wa Ubangiji. Ubangiji kuwa bai ƙara daure da azabar da Isra’ila suke sha ba.

  3. Shugabannin Isra’ila da sarki suka ƙasƙantar da kansu suka ce, “Ubangiji mai adalci ne.”

  4. Sa’ad da Ubangiji ya ga sun ƙasƙantar da kansu, sai wannan maganar Ubangiji ta zo wa Shemahiya, “Tun da yake sun ƙasƙantar da kansu, to, ba zan hallaka su ba, amma zan cece su, ba zan kwararo fushina ta hannun Shishak a kan Urushalima ba.

  5. Sau da yawa ya cece su, amma sun nace su yi tawaye suka kuma lalace cikin zunubinsu.

  6. Amma ya lura da wahalarsu sa’ad da ya ji kukansu;

  7. saboda su ya tuna da alkawarinsa kuma daga yawan ƙaunarsa ya ji tausayi.

  8. Ya sa aka ji tausayinsu a wurin dukan waɗanda suka kame su.

  9. Da Allah ya ga abin da suka yi, da kuma yadda suka juya daga mugayen hanyoyinsu sai ya ji tausayinsu, bai kawo hallaka a kansu yadda ya yi shirin yi ba.