Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da National Sins: Pervade all ranks

7 ayoyi · 34 fannoni

Ayoyi game da Pervade all ranks

  1. Me ya sa za a ƙara yin muku dūka? Me ya sa kuka nace ga yin tayarwa? An yi wa dukan kanku rauni, zuciyarku duk tana ciwo.

  2. “Ku yi ta kai da kawowa a titunan Urushalima, ku dudduba ko’ina ku kuma lura, ku bincika cikin dandalinta. Ko za ku sami mutum guda wanda yake aikata adalci wanda yake kuma son bin gaskiya, sai in gafarta wa wannan birni.

  3. Ko da yake suna cewa, ‘Muddin Ubangiji yana raye,’ duk da haka suna rantsuwar ƙarya.”

  4. Ya Ubangiji, idanunka ba sa ganin gaskiya? Ka buge su, amma ba su ji zafi ba; ka ragargaza su, amma suka ƙi su gyara. Fuskarsu ta ƙeƙashe fiye da dutse suka ƙi su tuba.

  5. Na yi tunani, “Waɗannan ne kawai matalauta; su wawaye ne, gama ba su san hanyar Ubangiji ba, ko abubuwan da Allahnsu yake bukata ba.

  6. Saboda haka zan tafi wurin shugabanni in yi musu magana; tabbatacce sun san hanyar Ubangiji, da abubuwan da Allahnsu yake bukata.” Amma da nufi guda su ma suka karye karkiyar suka tsintsinke sarƙoƙin.

  7. “Daga ƙarami zuwa babba, dukansu masu haɗama ne don riba; har da annabawa da firistoci, dukansu suna aikata rashin gaskiya.