Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert

759 ayoyi · 177 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Musa ya sa teburin a Tentin Sujada, a gefen arewa na tabanakul waje da labulen.

  2. Ya shirya burodin a kai a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  3. Ya sa wurin ajiye fitilan a Tentin Sujada ɗaura da teburin a gefen kudu na tabanakul

  4. ya kuma shirya fitilun a gaban Ubangiji, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  5. Musa ya sa bagaden zinariya a cikin Tentin Sujada a gaban labulen

  6. ya ƙone turare mai ƙanshi a kai, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  7. Sa’an nan ya sa labule a ƙofar shiga na tabanakul.

  8. Ya sa bagaden hadaya ta ƙonawa kusa da ƙofar tabanakul, Tentin Sujada, sa’an nan ya miƙa hadaya ta ƙonawa da hadaya ta gari a kansa, yadda Ubangiji ya umarce shi.

  9. Ya sa daro tsakanin Tentin Sujada da bagade, ya kuma zuba ruwa a cikinsa don wanki,

  10. a cikin kuwa Musa da Haruna da ’ya’yansa maza sukan wanke hannunsa da ƙafafunsu.

  11. Sukan yi wanka a duk sa’ad da suka shiga Tentin Sujada, ko in suka kusaci bagade, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  12. Sa’an nan Musa ya yi fili kewaye da tabanakul da kuma bagaden, ya rataye labule a ƙofar shiga filin. Da haka Musa ya gama aikin.

  13. Sa’an nan girgije ya rufe Tentin Sujada sai ɗaukakar Ubangiji ta cika tabanakul.

  14. Musa bai iya shiga Tentin Sujada ba domin girgije ya riga ya sauka a kansa, ɗaukakar Ubangiji kuwa ta cika tabanakul.

  15. Cikin tafiyar Isra’ilawa duka, sukan kama tafiyarsu ne a duk sa’ad da girgijen ya tashi daga kan tabanakul.

  16. Idan girgijen bai tashi ba, ba za su tashi ba, sai a ranar da ya tashi.

  17. Gama a cikin tafiyarsu duka, girgijen Ubangiji yana kan tabanakul da rana, da dare kuwa wuta yake cikinsa domin dukan Isra’ilawa su gani.

  18. Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,

  19. “Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi.

  20. Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja.

  21. Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.

  22. “Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;

  23. daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;

  24. daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;

  25. daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar;