Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Passover first commemorated
Ayoyi game da Passover first commemorated
Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai, a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar. Ya ce,
“Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.
A yi wannan bikin ƙayyadadden lokaci da yamma, a rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, a yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa.”
Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,
suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa.