Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Second numbering of the people

46 ayoyi · 177 fannoni

Ayoyi game da Second numbering of the people

  1. Ubangiji ya yi magana da Musa a Tentin Sujada a cikin Hamadar Sinai, a rana ta fari na watan biyu a shekara ta biyu, bayan Isra’ilawa suka fito Masar ya ce,

  2. “Ka yi ƙidayan dukan al’umman Isra’ilawa bisa ga iyalansu da kabilarsu, ka rubuta kowa da sunansa bi da bi.

  3. Da kai da Haruna za ku lissafta dukan mazan Isra’ila bisa ga sashensu, waɗanda suka kai shekaru ashirin ko fiye, da za su iya shiga soja.

  4. Mutum ɗaya daga kowace kabila wanda yake shugaban danginsa, zai taimake ku.

  5. “Ga sunayen da za su taimake ku. “Daga kabilar Ruben, Elizur ɗan Shedeyur;

  6. daga kabilar Simeyon, Shelumiyel ɗan Zurishaddai;

  7. daga kabilar Yahuda, Nashon ɗan Amminadab;

  8. daga kabilar Issakar, Netanel ɗan Zuwar;

  9. daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;

  10. daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;

  11. daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;

  12. daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai;

  13. daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;

  14. daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;

  15. daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.”

  16. Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.

  17. Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su,

  18. suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye,

  19. yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.

  20. Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  21. Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne.

  22. Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  23. Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne.

  24. Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  25. Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne.