Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Moses beholds Canaan

4 ayoyi · 177 fannoni

Ayoyi game da Moses beholds Canaan

  1. Sai Musa ya hau Dutsen Nebo daga filayen Mowab, zuwa ƙwanƙolin Fisga, wanda yake ƙetare Yeriko. A can Ubangiji ya nuna masa dukan ƙasar, daga Gileyad zuwa Dan,

  2. da ta dukan Naftali, da yankin Efraim da na Manasse, dukan ƙasar Yahuda har zuwa Bahar Rum,

  3. da Negeb da dukan yankin Kwarin Yeriko, Birnin Dabino, har zuwa Zowar.

  4. Sa’an nan Ubangiji ya ce masa, “Wannan ce ƙasar da na yi alkawari da rantsuwa wa Ibrahim, Ishaku da Yaƙub, sa’ad da na ce, ‘Zan ba da ita ga zuriyarku.’ Na bar ka ka gani da idanunka, amma ba za ka haye zuwa cikinta ba.”