Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Sabbath breaker stoned

5 ayoyi · 177 fannoni

Ayoyi game da Sabbath breaker stoned

  1. Yayinda Isra’ilawa suke ciki hamada, sai aka sami wani mutum yana tattara itace a ranar Asabbaci.

  2. Waɗanda suka gan shi, suka kawo shi wurin Musa da Haruna da dukan taro,

  3. sai suka sa shi a gidan waƙafi don ba su riga sun san abin da za a yi da shi ba tukuna.

  4. Sai Ubangiji ya ce wa Musa, “Dole mutumin yă mutu. Dole dukan taron su jajjefe shi a bayan sansani.”

  5. Saboda haka taron suka ɗauke shi zuwa bayan sansani, suka kuma jajjefe shi har ya mutu, yadda Ubangiji ya umarci Musa.