Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Flesh promised

12 ayoyi · 177 fannoni

Ayoyi game da Flesh promised

  1. Musa ya ji mutanen suna ta gunaguni ko’ina a cikin iyalansu, kowane mutum a ƙofar tentinsa. Ubangiji kuwa ya husata ƙwarai, sai Musa ya damu.

  2. Sai ya ce wa Ubangiji, “Me ya sa ka kawo wannan damuwar a kan bawanka? Me na yi da ya ɓata maka rai har ka ɗora dukan nauyin mutanen nan a kaina?

  3. Ni ne na yi cikin dukan mutanen nan? Ni ne na haife su? To, me ya sa ka ce in ɗauke su a ƙirjina kamar yadda mai reno yake rungume jariri, zuwa ƙasa wadda ka yi alkawari da rantsuwa za ka ba wa kakanninsu?

  4. Ina ne zan sami nama in waɗannan mutane? Sun dinga yin mini kuka suna cewa ‘Ka ba mu nama mu ci!’

  5. Ba zan iya ɗaukan dukan mutanen nan ni kaɗai ba, nauyin ya yi mini yawa.

  6. In haka za ka yi da ni, ka kashe ni yanzu, in na sami tagomashi daga gare ka, kada ka bar ni in rayu in ga wannan baƙin ciki.”

  7. “Ka gaya wa mutane, ‘Ku tsarkake kanku don gobe, za ku ci nama. Ubangiji ya ji ku sa’ad da kuka yi kuka cewa, “Da mun sami nama mun ci mana! Ai, da ba mu da damuwa, gama lokacin da muke zama cikin Masar ba mu da damuwa!” Yanzu Ubangiji zai ba ku nama, za ku kuma ci.

  8. Ba za ku ci shi na kwana ɗaya, ko biyu, ko biyar, ko goma, ko kuma kwana ashirin kaɗai ba,

  9. amma za ku ci har na wata guda cur, sai ya gundure ku a hanci har ku yi ƙyamarsa, domin kun ƙi Ubangiji wanda yake cikinku, kuka yi kuka a gabansa, kuna cewa, “Don me ma muka bar ƙasar Masar?” ’ ”

  10. Amma Musa ya ce, “Ga ni a cikin mutane dubu ɗari shida tafe tare da ni, kana kuma cewa, ‘Zan ba su nama su ci har wata guda cur!’

  11. Za su ma sami isashe in har aka yanka musu garkuna tumaki da na shanu? Za su sami isashe in aka kama musu dukan kifin teku?”

  12. Ubangiji ya ce wa Musa, “Akwai abin da ya fi ƙarfina ne? Bari ka gani ko abin da na ce zan yi, zai faru ko babu.”