Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Murmuring of the mixed multitude and of Israel, for flesh

6 ayoyi · 177 fannoni

Ayoyi game da Murmuring of the mixed multitude and of Israel, for flesh

  1. Wata rana, baƙin da suke cikinsu, suka fara kwaɗayin waɗansu abinci, har suka sa Isra’ilawa suka fara kuka, suna cewa, “Da mun sami nama mun ci mana!

  2. Mun tuna da kifin da muka ci kyauta a Masar, haka ma kayan lambu irin su kukumba, guna, safa, albasa da kuma tafarnuwa.

  3. Amma ga shi yanzu ba mu da wani abin marmari; in ba wannan Manna ba!”

  4. Manna kuwa kamar tsabar riɗi take, kamanninta kuma kamar ƙaro ne.

  5. Mutane sukan fita su tattara ta, su niƙa a dutsen niƙa, ko kuwa su daka a turmi. Su dafa, ko su yi waina da ita. Ɗanɗanonta yakan yi kamar abin da aka yi da man zaitun.

  6. Sa’ad da raɓa tana saukowa da dad dare a kan sansani, Manna ma takan sauko.