Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: The Amorites refuse a passage to Israel

8 ayoyi · 177 fannoni

Ayoyi game da The Amorites refuse a passage to Israel

  1. Isra’ila suka aiki manzanni wurin Sihon sarkin Amoriyawa su ce,

  2. “Ka bari mu ratsa ta ƙasarka. Ba za mu shiga wata gona ba, ba za mu kuma shiga gonar inabi, ko mu sha ruwa daga wata rijiya ba. Za mu bi ta babbar hanyar sarki, har mu fita ƙasarka.”

  3. Amma Sihon bai bar Isra’ila su ratsa ta yankinsa ba. Sai ya tara dukan sojojinsa, suka fita zuwa cikin hamada, su yaƙi Isra’ila. Da ya kai Yahaz, sai ya yaƙi Isra’ila.

  4. Daga hamadar Kedemot, na aiki ’yan saƙo zuwa wurin Sihon sarkin Heshbon, a kan ina neman zaman lafiya, ina cewa,

  5. “Bari mu wuce cikin ƙasarka. Za mu bi ta kan hanya ne kaɗai; ba za mu ratse dama ko hagu ba.

  6. Ka sayar mana da abincin da za mu ci, da kuma ruwan da za mu sha a farashinsu na azurfa. Ka dai bar mu mu wuce ta ƙasarka kawai,

  7. kamar yadda zuriyar Isuwa, waɗanda suke zaune a Seyir, da Mowabawa, waɗanda suke zaune a Ar, suka yardar mana, gama muna so mu ƙetare Urdun zuwa ƙasa wadda Ubangiji, Allahnmu yake ba mu.”

  8. Amma Sihon sarkin Heshbon ya ƙi yă bar mu mu wuce a ciki. Gama Ubangiji Allahnku ya sa ruhunsa ya taurare don yă ba da shi a hannuwanku kamar yadda ya yi yanzu.