- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert: Judges appointed
Ayoyi game da Judges appointed
Sa’ad da surukinsa ya lura da duk abin da Musa yake yi saboda mutane, sai ya ce, “Mene ne wannan da kake yi wa mutane? Don me kai kaɗai kake zama kana yin shari’a wa mutane, yayinda mutanen nan suke tsaya kewaye da kai daga safe har yamma?”
Musa ya amsa ya ce, “Saboda mutanen suna zuwa wurina, don su nemi nufin Allah.
Duk lokacin da suke da gardama, akan kawo su a wurina, ni kuma sai in raba tsakaninsu, in kuma koya musu dokokin Allah da farillansa.”
Surukin Musa ya amsa ya ce, “Abin da kake yi ba daidai ba ne.
Kai da dukan mutanen da suke zuwa wurinka za ku gajiyar da kanku. Aikin ya fi ƙarfinka; ba za ka iya yinsa kai kaɗai ba.
Ka kasa kunne gare ni yanzu, zan ba ka shawara, Allah kuma yă kasance tare da kai. Kai za ka zama wakilin mutane a gaban Allah, ka kuma kawo gardamansu gare shi.
Ka koya musu dokokinsa da farillarsa, ka kuma nuna musu hanyar rayuwa da ayyukan da za su yi.
Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.
Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.
In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”
Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa.
Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.
Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu.
A wancan lokaci na faɗa muku cewa, “Ku kaya ne masu nauyi da ni kaɗai ba zan iya ɗauka ba.
Ubangiji Allahnku ya ƙara yawanku har yau kuka zama da yawa kamar taurari a sarari.
Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari!
Amma yaya zan ɗauka dukan damuwoyinku da nawayarku da kuma faɗace-faɗacenku duka ni kaɗai?
Ku zaɓi waɗansu masu hikima, masu ganewa, da kuma mutanen da ake girmama daga kowace kabilarku, zan kuma sa su a kanku.”
Kuka amsa mini, kuka ce, “Abin da ka ce za ka yi, yana da kyau.”
Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.