Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
daga kabilar Zebulun, Eliyab ɗan Helon;
daga kabilar ’ya’yan Yusuf, daga Efraim, Elishama ɗan Ammihud; daga Manasse, Gamaliyel ɗan Fedazur;
daga kabilar Benyamin, Abidan ɗan Gideyoni;
daga kabilar Dan, Ahiyezer ɗan Ammishaddai;
daga kabilar Asher, Fagiyel ɗan Okran;
daga kabilar Gad, Eliyasaf ɗan Deyuwel;
daga kabilar Naftali, Ahira ɗan Enan.”
Waɗannan su ne mutanen da aka naɗa daga cikin jama’a, shugabannin asalin kabilu. Su ne kuma shugabannin dangogin Isra’ila.
Sai Musa da Haruna suka ɗauki sunayen mutanen nan da aka ba su,
suka kira dukan al’umma wuri ɗaya a rana ta fari ga wata na biyu. Aka kuwa rubuta mutanen bisa ga asalin kabilansu da iyalansu. Aka kuma rubuta sunayen maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekaru ashirin ko fiye,
yadda Ubangiji ya umarci Musa. Da haka ya ƙidaya su a Hamadar Sinai.
Daga zuriyar Ruben ɗan fari na Isra’ila. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Ruben 46,500 ne.
Daga zuriyar Simeyon. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Simeyon 59,300 ne.
Daga zuriyar Gad. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Gad 45,650 ne.
Daga zuriyar Yahuda. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Yahuda 74,600 ne.
Daga zuriyar Issakar. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Issakar 54,400 ne.
Daga zuriyar Zebulun. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Zebulun 57,400 ne.
Daga ’ya’yan Yusuf. Daga zuriyar Efraim. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.
Jimillar maza daga mutanen Efraim 40,500 ne.