Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert

759 ayoyi · 177 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Daga zuriyar Manasse. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  2. Jimillar maza daga mutanen Manasse 32,200 ne.

  3. Daga zuriyar Benyamin. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  4. Jimillar maza daga mutanen Benyamin 35,400 ne.

  5. Daga zuriyar Dan. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  6. Jimillar maza daga mutanen Dan 62,700 ne.

  7. Daga zuriyar Asher. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  8. Jimillar maza daga mutanen Asher 41,500 ne.

  9. Daga zuriyar Naftali. Aka rubuta sunayen dukan maza ɗaya-ɗaya da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, bisa ga iyalansu da kabilarsu da take a rubuce.

  10. Jimillar maza daga mutanen Naftali kuwa 53,400 ne.

  11. Waɗannan su ne mazan da Musa da Haruna, tare da shugabanni goma sha biyun nan na Isra’ila suka ƙidaya, kowa a madadin iyalinsa.

  12. Dukan Isra’ilawan da suka kai shekara ashirin ko fiye da suka isa shiga soja, an ƙidaya su bisa ga iyalansu.

  13. Jimillar kuwa ita ce mutum 603,550.

  14. Ubangiji ya ce wa Musa da Haruna,

  15. “Duk sa’ad da Isra’ilawa suka yi sansani, kowane mutum zai sauka a inda tutar ƙungiyar kabilarsa take. Sansanin zai kasance a kewaye da Tentin Sujada.”

  16. Kabilar Yahuda za su yi sansani bisa ga ƙa’idarsu a gabas, wajen fitowar rana. Shugaban mutanen Yahuda kuwa shi ne Nashon ɗan Amminadab.

  17. Yawan mutanen sashensa 74,600 ne.

  18. Kabilar Issakar za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Netanel ɗan Zuwar.

  19. Yawan mutanen sashensa 54,400 ne.

  20. Kabilar Zebulun za su yi sansani biye da su. Shugabansu shi ne Eliyab ɗan Helon.

  21. Yawan mutanen sashensa 57,400 ne.

  22. Dukan mazan da aka ba su aiki a sansanin Yahuda bisa ga sashensu sun kai 186,400. Su ne za su ja gaba.

  23. A kudu, a nan ne sashe sansanin mutanen Ruben a ƙarƙashin ƙa’idarsu, za su yi sansani. Shugaban mutanen Ruben shi ne Elizur ɗan Shedeyur.

  24. Yawan mutanen sashensa 46,500 ne.

  25. Kabilar Simeyon za su yi sansani biye da su. Shugaban mutanensa shi ne Shelumiyel ɗan Zurishaddai.