Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Journey of Israel Through The Desert

759 ayoyi · 177 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ubangiji ya ce wa Musa,

  2. “Ka kawo mutanen Lawi, ka kuma gabatar da su ga Haruna firist, don su taya shi aiki.

  3. Za su yi wa Haruna da dukan al’umma aikace-aikace a Tentin Sujada, ta wurin yin aikin tabanakul.

  4. Za su lura da dukan kayayyakin Tentin Sujada, suna cika hakkin Isra’ilawa ta wurin yin aiki a tabanakul.

  5. Ka ba da Lawiyawa ga Haruna da ’ya’yansa; su ne za su zama Isra’ilawan da za a ba da su ɗungum gare shi.

  6. Ubangiji ya kuma ce wa Musa,

  7. “Ga shi na ɗauki Lawiyawa daga cikin Isra’ilawa a maimakon ɗan fari na kowace mace a Isra’ila. Lawiyawa nawa ne,

  8. gama duk ’ya’yan fari nawa ne. Lokacin da karkashe duk ’ya’yan fari a Masar, na keɓe wa kaina kowane ɗan fari a Isra’ila, ko mutum, ko dabba. Za su zama nawa. Ni ne Ubangiji.”

  9. Ubangiji ya yi magana da Musa a Hamadar Sinai, a watan farko na shekara ta biyu bayan fitarsu daga ƙasar Masar. Ya ce,

  10. “Ka sa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa a ƙayyadadden lokaci.

  11. A yi wannan bikin ƙayyadadden lokaci da yamma, a rana ta goma sha huɗu ga wannan wata, a yi shi bisa ga dokokinsa da ƙa’idodinsa.”

  12. Saboda haka sai Musa ya gaya wa Isra’ilawa su yi Bikin Ƙetarewa,

  13. suka kuwa yi haka a Hamadar Sinai da yamma, a rana ta sha huɗu ga watan farko. Isra’ilawa suka yi dukan abubuwa yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  14. Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba.

  15. Netanel ɗan Zuwar ne shugaban ɓangaren kabilar Issakar,

  16. Eliyab ɗan Helon kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Zebulun.

  17. Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya.

  18. Sai ɓangarori sansanin Ruben suka biyo, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Elizur ɗan Shedeyur ne shugaba.

  19. Shelumiyel ɗan Zurishaddai ne shugaban ɓangaren kabilar Simeyon,

  20. Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad.

  21. Sai Kohatawa suka kama hanya, ɗauke da kayayyaki masu tsarki, domin kafin su kai wurin da za a kafa sansani, a riga an kafa tabanakul.

  22. Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba.

  23. Gamaliyel ɗan Fedazur ne shugaban ɓangaren kabilar Manasse,

  24. Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin.

  25. A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba.