Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idolatry

447 ayoyi · 205 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Yanzu sai yin zunubi a kai a kai suke; suna yin gumaka wa kansu daga azurfansu, da wayo suna sarrafa siffofi, dukansu aikin masu aikin hannu ne. Ana magana waɗannan mutane cewa, “Suna miƙa hadayar mutum su kuma sumbaci gumakan maruƙa.”

  2. Saboda haka za su zama kamar hazon safiya, kamar raɓar safen da yakan kakkaɓe, kamar ƙaiƙayin da ake tankaɗe daga masussuka, kamar hayaƙin da yake fita daga taga.

  3. “Amma ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar. Ba za ku yarda da wani Allah ba sai ni, ba wani Mai Ceto in ban da ni.

  4. “Ku tafi Betel ku yi ta aikata zunubi; ku je Gilgal ku ƙara yin zunubi. Ku kawo hadayunku kowace safiya, zakkarku kowace shekara uku.

  5. Ku ƙona burodinku mai yisti kamar hadaya ta godiya, ku yi fariya game da hadayunku na yarda rai, ku yi taƙama game da su, ya ku Isra’ilawa, gama abin da kuke jin daɗin aikata ke nan,” in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  6. Maganar Ubangiji ta zo wa Mika mutumin Moreshet a zamanin Yotam, da na Ahaz, da kuma na Hezekiya, sarakunan Yahuda, Mika ya ga wahayi a kan Samariya da kuma a kan Urushalima. Ga abin da ya ce.

  7. Ku ji, ya ku mutane duka, ki saurara, ya ke duniya da dukan mazauna cikinki, bari Ubangiji Mai Iko Duka yă zama shaida a kanku, daga haikalinsa mai tsarki.

  8. Duba! Ubangiji yana zuwa daga wurin zamansa; zai sauko yă taka maɗaukakan wuraren duniya.

  9. Duwatsu za su narke a ƙarƙashin ƙafafunsa, kamar kaki a gaban wuta, kwaruruka kuma za su ɓace, kamar ruwan da yake gangarowa daga tsauni.

  10. Duk wannan zai faru saboda laifin Yaƙub, da kuma zunuban gidan Isra’ila ne. Mene ne laifin Yaƙub? Shin, ba Samariya ba ce? Ina ne maɗaukakan wuraren Yahuda? Shin, ba Urushalima ba ce?

  11. “Saboda haka zan mai da Samariya tarin juji, wurin noman inabi. Zan zubar da duwatsunta a cikin kwari in kuma bar harsashin gininta a bayyane.

  12. Za a ragargaje dukan allolinta; za a ƙone dukan baye-bayenta na haikali da wuta; zan lalatar da dukan gumakanta. Tun da ta wurin karuwanci ne ta tattara su, ga karuwanci kuma za su koma.”

  13. Saboda wannan zan yi baƙin ciki, in yi kuka; zan yi tafiya ba takalmi, zan tuɓe, in kuma yi tafiya tsirara. Zan yi kuka kamar dila, in yi baƙin ciki kamar mujiya.

  14. Gama raunin Samariya ba mai warkewa ba ne; ya bazu har Yahuda. Ya ma kai bakin ƙofar mutanena, har ma Urushalima da kanta.

  15. Zan kawar da maitarku, ba za a ƙara yin sihiri ba.

  16. Zan sassare dukan gumakan da kuka sassaƙa da keɓaɓɓun duwatsunku a cikinku, nan gaba ba za ku ƙara rusuna wa aikin hannuwanku ba.

  17. Zan tumɓuke daga gare ku ginshiƙan Asheranku in kuma rurrushe biranenku.

  18. “Ina amfanin gunki da mutum ne ya sassaƙa? Ko siffar da take koyar da ƙarya? Gama wanda ya yi shi yana dogara ne ga halittarsa; ya yi gumakan da ba sa magana.

  19. Kaito wanda ya ce da katako, ‘Rayu!’ Ko kuwa dutse marar rai, ‘Farka!’ Zai iya bishewa ne? An dalaye shi da zinariya da azurfa; ba numfashi a cikinsa.”

  20. Yahuda ya ci amana. An yi abin kunya a Isra’ila da kuma a Urushalima. Yahuda ya ƙazantar da wuri mai tsarkin da Ubangiji yake ƙauna, ta wurin auren ’yar wani baƙon allah.

  21. Game da mutumin da ya aikata wannan, ko wane ne shi, bari Ubangiji yă yanke shi daga tentunan Yaƙub, ko da ma ya kawo hadayu ga Ubangiji Maɗaukaki.

  22. Ga kuma wani abin da kuke yi. Kukan cika bagaden Ubangiji da hawaye. Kukan yi kuka kuna ihu gama Ubangiji ba ya mai da hankali ga hadayunku ko yă karɓe su da farin ciki.

  23. Ya ce, “Zan ba ka dukan wannan, in za ka durƙusa ka yi mini sujada.”

  24. Sai Yesu ya ce masa, “Rabu da ni, Shaiɗan! Gama a rubuce yake, ‘Yi wa Ubangiji Allahnka sujada, shi kaɗai kuma za ka bauta wa.’”

  25. “Amma kakanninmu suka ƙi yin masa biyayya. A maimakon haka, sai suka ƙi shi a cikin zuciyarsu kuwa suka koma Masar.