Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idolatry: Folly of

77 ayoyi · 205 fannoni

Ayoyi game da Folly of

Tace bisa littafi
  1. Zai ce, “To, ina allolinsu, dutsen da suka yi mafaka a ciki,

  2. allolin da suka ci kitsen hadayunsu suka kuma sha ruwan inabin hadayunsu? Ku sa su tashi su taimake ku mana! Bari su ba ku mafaka!

  3. Kashegari da safe da mutanen Ashdod suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a gaban akwatin alkawarin Ubangiji. Sai suka ɗauki Dagon suka ajiye a wurin zamansa.

  4. Amma kashegari kuma da safe suka farka sai ga Dagon ya fāɗi a ƙasa a gaban akwatin alkawarin Ubangiji! Kansa ya fashe, hannuwansa kuma sun kakkarye sun zube a madogarar ƙofa; jikinsa ne kaɗai ya rage.

  5. Cikin lokacin wahalarsa Sarki Ahaz ya ƙara zama marar aminci ga Ubangiji.

  6. Ya miƙa hadayu ga allolin Damaskus, waɗanda suka ci shi a yaƙi; gama ya yi tunani, “Da yake allolin sarakunan Aram sun taimake su, zan miƙa hadayu domin su taimake ni.” Amma suka zama sanadin fāɗuwarsa da kuma fāɗuwar dukan Isra’ila.

  7. Amma gumakansu azurfa da zinariya ne, da hannuwan mutane suka yi.

  8. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;

  9. Gumakan al’ummai azurfa ne da zinariya, da hannuwan mutane suka yi.

  10. Suna da bakuna, amma ba sa magana, idanu, amma ba sa gani;

  11. suna da kunnuwa, amma ba sa ji, ba kuwa numfashi a bakunansu.

  12. Waɗanda suka yi su za su zama kamar su, haka kuma zai zama da dukan waɗanda suke dogara gare su.

  13. Wane ne ya auna ruwaye a tafin hannunsa, ko kuwa ya gwada tsawon sammai da fāɗin tafin hannunsa? Wane ne ya riƙe ƙurar ƙasa a kwando, ko kuwa ya auna nauyin duwatsu a magwaji, tuddai kuma a ma’auni?

  14. Wane ne ya fahimci zuciyarUbangiji, ko kuwa ya koya masa a matsayin mashawarcinsa?

  15. Wane ne Ubangiji ya nemi shawararsa don yă ganar da shi, wane ne kuma ya koya masa hanyar da ta dace? Wane ne ya koya masa sani ko ya nuna masa hanyar fahimta?

  16. Tabbatacce al’ummai suna kama da ɗigon ruwa a cikin bokiti an ɗauke su a matsayin ƙura a kan magwaji; yakan auna tsibirai sai ka ce ƙura mai laushi.

  17. Itatuwan Lebanon ba su isa a yi wutar bagade da su ba, balle dabbobinsa su isa yin hadayun ƙonawa.

  18. A gabansa dukan al’ummai ba kome ba ne; ya ɗauke su ba a bakin kome ba kuma banza ne kurum.

  19. To, ga wane ne za ka kwatanta Allah? Wace siffa za ka kwatanta shi da ita?

  20. Gunki dai, maƙeri kan yi zubinsa, maƙerin zinariya kuma yă ƙera shi da zinariya yă kuma sarrafa masa sarƙoƙin azurfa.

  21. Mutumin da talauci ya sha kansa da ba zai iya miƙa irin hadayar nan ba kan zaɓi itacen da ba zai ruɓe ba. Yakan nemi gwanin sassaƙa don yă sassaƙa masa gunkin da ba zai fāɗi ba.

  22. Ba ku sani ba? Ba ku taɓa ji ba? Ba a faɗa muku daga farko ba? Ba ku fahimta ba tun kafawar duniya?

  23. Yana zaune a kursiyi a bisa iyakar duniya, kuma mutanenta suna kama da fāra. Ya miƙa sammai kamar rumfa, ya kuma shimfiɗa su kamar tentin da za a zauna a ciki.

  24. Yakan mai da sarakuna ba kome ba yă mai da masu mulkin wannan duniya wofi.

  25. Ba da jimawa ba bayan an shuka su, ba da jimawa ba bayan an dasa su, ba da jimawa ba bayan sun yi saiwa a ƙasa, sai yă hura musu iska su yanƙwane, guguwa kuma ta kwashe su kamar yayi.