Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idolatry: Captivity of Judah on account of

5 ayoyi · 205 fannoni

Ayoyi game da Captivity of Judah on account of

  1. ko Yahuda ma ba su kiyaye umarnan Ubangiji Allahnsu ba. Sun bi gurbin da Isra’ila ta kawo.

  2. Saboda haka Ubangiji ya wofinta mutanen Isra’ila; ya azabtar da su, ya kuma ba da su a hannun masu kwasar ganima, sai da ya shafe su ƙaƙaf daga gabansa.

  3. Sa’ad da ya ware Isra’ila daga gidan Dawuda, sai suka naɗa Yerobowam ɗan Nebat sarki a kansu. Yerobowam ya rinjayi Isra’ila daga ƙin Ubangiji, ya sa suka aikata babban zunubi.

  4. Isra’ila suka nace cikin dukan zunuban Yerobowam, ba su kuwa rabu da su ba

  5. har Ubangiji ya kawar da su daga gabansa, kamar yadda ya gargaɗe su ta bakin bayinsa annabawa. Saboda haka aka kwashi mutanen Isra’ila daga ƙasarsu zuwa bauta a Assuriya, har wa yau kuwa suna can.