Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idolatry: Banishment
Ayoyi game da Banishment
Ku zubar da gunkin maraƙinku, ya Samariya! Fushina yana ƙuna a kansu. Sai yaushe za su rabu da gumaka?
Su daga Isra’ila ne! Wannan maraƙi, mai aikin hannu ne ya yi shi; gunki ne ba Allah ba. Za a farfashe shi kucu-kucu, waccan maraƙin Samariya.
“Gama sun shuka iska don haka za su girbe guguwa. Hatsin da yake tsaye ba shi da kai, ba zai yi tsaba ba. Ko da ya yi tsaba ma, baƙi ne za su ci.
An haɗiye Isra’ila; yanzu tana cikin al’ummai kamar abin da ba shi da amfani.