Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Idolatry

447 ayoyi · 205 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ko da yake sun sayar da kansu a cikin al’ummai, yanzu zan tattara su wuri ɗaya. Za su fara lalacewa a ƙarƙashi danniyar babban sarki.

  2. “Ko da yake Efraim ya gina bagadai masu yawa don hadayun zunubi, waɗannan sun zama bagade don yin zunubi.

  3. Na rubuta musu abubuwa masu yawa na dokata, amma suka ɗauke su tamƙar wani baƙon abu ne.

  4. Suna miƙa hadayun da aka ba ni su kuma ci nama, amma Ubangiji ba ya jin daɗinsu. Yanzu zai tuna da muguntarsu yă kuma hukunta zunubansu. Za su koma Masar.

  5. Isra’ila ya manta da Mahaliccinsa ya kuma gina fadodi; Yahuda ya gina katanga a yawancin garuruwansa. Amma zan aiko da wuta a bisa biranensu da zai cinye kagaransu.”

  6. Isra’ila kuringa ce mai yaɗuwa; ya fitar da ’ya’ya wa kansa. Yayinda ’ya’yan suka ƙaru, ya gina ƙarin bagadai; da ƙasarsa ta wadata, ya yi wa keɓaɓɓun duwatsu ado.

  7. Zuciyarsu masu ruɗu ne, yanzu kuwa dole su ɗauki laifinsu. Ubangiji zai rushe bagadansu yă kuma hallaka keɓaɓɓun duwatsunsu.

  8. Sa’an nan za su ce, “Ba mu da sarki domin ba mu girmama Ubangiji ba. Amma ko da ma muna da sarki, me zai yi mana?”

  9. Sun yi alkawura masu yawa, suka yi rantsuwar ƙarya da kuma yarjejjeniyoyi; saboda haka ƙararraki suka taso kamar ciyayi masu dafi da aka nome a gona.

  10. Mutanen da suke zama a Samariya suna tsoro saboda gunki maraƙin Bet-Awen. Mutanensa za su yi makokinsa, haka ma firistocinsa matsafa, waɗanda suka yi farin ciki a kan darajarsa, don an ɗauke ta daga gare su aka kai ta zaman bauta.

  11. Za a ɗauke shi a kai Assuriya kamar gandu wa babban sarki. Efraim zai sha kunya; Isra’ila zai sha kunya saboda gumakan itacensa.

  12. Samariya da sarkinta za su ɓace kamar kumfa a bisa ruwaye.

  13. Za a hallaka masujadai kan tudu na mugunta zunubin Isra’ila ne. Ƙayayuwa da sarƙaƙƙiya za su yi girma su rufe bagadansu. Sa’an nan za su ce wa duwatsu, “Ku rufe mu!” Ga tuddai kuma, “Ku fāɗo a kanmu!”

  14. “Tun daga kwanakin Gibeya, kun yi zunubi, ya Isra’ila, a can kuwa kuka ci gaba. Yaƙi bai cimma masu aikata mugunta a Gibeya ba?

  15. Sa’ad da na ga dama, zan hukunta su; al’ummai za su taru su yi gāba da su don su daure su saboda zunubansu da suka riɓanya.

  16. Efraim horarriyar karsana ce mai son sussuka; saboda haka zan sa karkiya a kyakkyawan wuyanta. Zan bi da Efraim, Dole Yahuda yă yi noma, dole kuma Yaƙub yă ja garman noma.

  17. Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.

  18. Amma kun shuka mugunta, kuka girbe mugu kuka ci ’ya’yan ruɗu. Domin kun dogara da ƙarfinku da kuma a jarumawanku masu yawa,

  19. hayaniyar yaƙi za tă tashi gāba da mutanenku, saboda a ragargaza kagaranku, kamar yadda Shalman ya ragargaza Bet-Arbel a ranar yaƙi, sa’ad da aka fyaɗa uwaye tare da ’ya’yansu da ƙasa.

  20. Haka zai faru da kai, ya Betel, domin muguntarka ta yi yawa. Sa’ad da wannan rana ta zo, za a hallaka sarkin Isra’ila ƙaƙaf.

  21. Gileyad mugu ne? Mutanensa mutanen banza ne! Suna miƙa bijimai a Gilgal? Bagadansu za su zama tsibin duwatsu. A gonar da aka nome.

  22. Yaƙub ya gudu zuwa ƙasar Aram; Isra’ila ya yi bauta don yă sami mata, domin kuma yă biya, sai da ya yi kiwon tumaki.

  23. Ubangiji ya yi amfani da annabi don yă fitar da Isra’ila daga Masar ta wurin annabi ya lura da shi.

  24. Amma Efraim ya yi muguwar tsokana da ta sa ya yi fushi; shugabansa zai ɗora musu hakkin jini a kansa kuma zai sāka masa saboda wulaƙancinsa.

  25. Sa’ad da Efraim ya yi magana, mutane sun yi rawan jiki; an girmama shi a cikin Isra’ila. Amma sai ya zama mai laifi na yin wa Ba’al sujada, ya kuwa mutu.