Tsallake zuwa abun ciki

circa 1900–1700 BC

Jacob, Joseph & Egypt

Jacob wrestles with God and becomes Israel; Joseph is sold into slavery yet rises to save the world from famine.

840 ayoyi · 1 littafi da aka rufe

Ayoyi daga wannan lokacin

  1. Farawa 40:21kusan 1717 K.H.

    Ya mai da shugaban masu shayarwa a matsayinsa, saboda haka shugaban masu shayarwa ya sāke sa kwaf a hannun Fir’auna,

  2. Farawa 40:22kusan 1717 K.H.

    amma ya rataye shugaban masu tuya, kamar dai yadda Yusuf ya faɗa musu a fassarar mafarkan da suka yi.

  3. Farawa 40:23kusan 1717 K.H.

    Shugaban masu shayarwa fa, bai tuna da Yusuf ba; ya mance da shi.

  4. Farawa 41:1kusan 1715 K.H.

    Bayan shekaru biyu cif, Fir’auna ya yi mafarki. A mafarkin, ya ga yana tsaye kusa da Nilu,

  5. Farawa 41:2kusan 1715 K.H.

    sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro.

  6. Farawa 41:3kusan 1715 K.H.

    Bayansu, sai ga waɗansu shanu bakwai, munana, ramammu, suka fito daga Nilu, suka tsaya kusa da waɗancan masu ƙiban, a bakin kogin.

  7. Farawa 41:4kusan 1715 K.H.

    Shanun nan da suke munana ramammu, suka cinye shanu bakwai nan masu ƙiba mulmul. Sai Fir’auna ya farka.

  8. Farawa 41:5kusan 1715 K.H.

    Ya sāke yin barci, sai ya yi mafarki na biyu; ya ga kawuna bakwai na dawa, ƙosassu masu kyau, suka yi girma a kara guda.

  9. Farawa 41:6kusan 1715 K.H.

    Bayansu, sai ga waɗansu kawuna bakwai na dawa, suka fito sirara waɗanda iskar gabas ta sa suka yanƙwane.

  10. Farawa 41:7kusan 1715 K.H.

    Siraran dawan suka haɗiye kawuna bakwai nan ƙosassu masu kyau. Sai Fir’auna ya farka, ashe, mafarki ne.

  11. Farawa 41:8kusan 1715 K.H.

    Da safe sai hankalinsa ya tashi, saboda haka sai ya aika a kawo dukan masu duba da masu hikima na Masar. Fir’auna ya faɗa musu mafarkansa, amma babu wanda ya iya ba shi fassararsu.

  12. Farawa 41:9kusan 1715 K.H.

    Sai shugaban masu shayarwa ya ce wa Fir’auna, “Yau an tuna mini da kāsawata.

  13. Farawa 41:10kusan 1715 K.H.

    Sai ya ci gaba ya ce, Fir’auna ya taɓa husata da bayinsa, ya kuma jefa ni da shugaban masu tuya a cikin kurkuku a gidan shugaban masu tsaro.

  14. Farawa 41:11kusan 1715 K.H.

    Kowannenmu ya yi mafarki a wani dare, kowane mafarki kuma ya kasance da ma’anarsa.

  15. Farawa 41:12kusan 1715 K.H.

    To, wani saurayi, mutumin Ibraniyawa ya kasance a can tare da mu, bawan shugaban masu tsaro. Sai muka faɗa masa mafarkanmu, ya kuwa fassara mana su, yana ba wa kowane mutum fassarar mafarkinsa.

  16. Farawa 41:13kusan 1715 K.H.

    Abubuwan kuwa suka kasance daidai yadda ya fassara su gare mu; aka mai da ni a matsayina, ɗaya mutumin kuwa aka rataye shi.”

  17. Farawa 41:14kusan 1715 K.H.

    Sai Fir’auna ya aika a kawo Yusuf, aka kuwa kawo shi da sauri daga kurkuku. Sa’ad da ya yi aski, ya kuma canja tufafinsa, sai ya zo gaban Fir’auna.

  18. Farawa 41:15kusan 1715 K.H.

    Fir’auna ya ce wa Yusuf, “Na yi mafarki, kuma babu wanda ya iya fassara shi. Amma na ji an ce sa’ad da ka ji mafarki, kana iya fassara shi.”

  19. Farawa 41:16kusan 1715 K.H.

    Yusuf ya amsa wa Fir’auna ya ce, “Ba ni ne da iyawar ba, Allah zai iya ba wa Fir’auna amsar da yake nema.”

  20. Farawa 41:17kusan 1715 K.H.

    Sa’an nan Fir’auna ya ce wa Yusuf, “A cikin mafarkina, na ga ina tsaye a bakin Nilu,

  21. Farawa 41:18kusan 1715 K.H.

    sai ga shanu bakwai masu ƙiba mulmul, suka fito daga kogin, suna kiwo a cikin kyauro.

  22. Farawa 41:19kusan 1715 K.H.

    Bayansu kuma, sai ga waɗansu shanu bakwai suka fito ƙanjamammu, munana, ramammu. Ban taɓa ganin irin munanan shanu haka a cikin dukan ƙasar Masar ba.

  23. Farawa 41:20kusan 1715 K.H.

    Ramammun shanun nan munana, suka cinye shanun nan bakwai masu ƙiba da suka fito da fari.

  24. Farawa 41:21kusan 1715 K.H.

    Amma ko bayan da suka cinye su, babu wanda zai iya faɗa cewa sun yi haka; suna nan dai munana kamar yadda suke a dā. Sai na farka.

  25. Farawa 41:22kusan 1715 K.H.

    “Har yanzu kuma, a cikin mafarkina na ga kawuna bakwai na dawa ƙosassu masu kyau, suna girma a kara guda.