Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ƙafafunsa sun kai shi cikin raga, yana ta yawo a cikin ragar.

  2. Tarko ya kama ɗiɗɗigensa; tarko ya riƙe shi kam.

  3. An ɓoye masa igiya da za tă zarge shi a ƙasa; an sa masa tarko a kan hanyar da zai bi.

  4. Tsoro duk ya kewaye shi ta kowane gefe yana bin shi duk inda ya je.

  5. Masifa tana jiransa; bala’i yana shirye yă fāɗa masa a lokacin da zai fāɗi.

  6. Ya cinye wani sashe na gaɓar jikinsa; ɗan fari na mutuwa ya cinye ƙafafunsa.

  7. An yage shi daga zaman lafiyar da yake yi a cikin tentinsa aka sa shi tsoro sosai.

  8. Wuta ta cinye tentinsa; farar wuta ta rufe wurin da yake zama.

  9. Jijiyoyinsa sun bushe a ƙasa rassansa sun mutu a sama.

  10. An manta da shi a duniya; ba wanda yake ƙara tunawa da shi.

  11. An tura shi daga cikin haske zuwa cikin duhu, an kore shi daga duniya.

  12. Ba shi da ’ya’ya ko zuriya cikin mutanensa, ba sauran wanda yake a raye a wurin da ya taɓa zama.

  13. Mutanen Yamma suna mamakin abin da ya faru da shi; tsoro ya kama mutanen gabas.

  14. Ba shakka haka wurin zaman mugun mutum yake, haka wurin zaman wanda bai san Allah ba yake.”

  15. mugun mutum bai taɓa daɗewa ba, farin cikin mutum na ɗan gajeren lokaci ne.

  16. Ko da ya ƙasaita ya kai sararin sama, kansa kuma yana taɓa gizagizai.

  17. Zai hallaka har abada, kamar bayan gidansa; waɗanda suka gan shi za su ce, ‘Ina yake?’

  18. Kamar mafarki haka zai ɓace, ba za a ƙara ganinsa ba zai ɓace kamar wahayi da dare.

  19. Idon da ya gan shi ba zai ƙara ganinsa ba; wurin zamansa ba zai sāke ganinsa ba.

  20. Dole ’ya’yansa su mayar wa matalauta abin da ya kamata; dole hannuwansa su mayar da dukiyarsa.

  21. Jin ƙarfi da ya cika ƙasusuwansa zai kwantar da shi a cikin ƙura.

  22. “Ko da yake mugunta tana da daɗi a bakinsa kuma yana ɓoye ta a harshensa,

  23. ko da yake ba zai iya rabuwa da ita ba, yana kuma ajiye ta a bakinsa,

  24. duk da haka abincin da ya ci zai zama da tsami a cikin cikinsa; zai zama kamar dafin maciji a cikinsa.

  25. Zai haras da dukiyar da ya haɗiye; Allah zai sa cikinsa yă haras da su.