Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked: Contrasted with the righteous

146 ayoyi · 18 fannoni

Ayoyi game da Contrasted with the righteous

Tace bisa littafi
  1. Mai farin ciki ne mutumin da ba ya aiki da shawarar mugaye ko yă yi abin da masu zunubi suke yi ko yă zauna tare da masu yin ba’a.

  2. Amma yana jin daɗin bin dokar Ubangiji, kuma yana ta nazarinta dare da rana.

  3. Yana kama da itacen da aka shuka kusa da maɓulɓulan ruwa, wanda yake ba da amfani a daidai lokaci wanda kuma ganyensa ba sa bushewa. Duk abin da yake yi, yakan yi nasara.

  4. Ba haka yake da mugaye ba! Su kamar yayi ne da iska take kwashewa.

  5. Saboda haka mugaye ba za su iya tsayawa a shari’a ba, balle a sami masu zunubi a taron adalai.

  6. Gama Ubangiji yana lura da yadda adalai suke yin abubuwa, amma ayyukan mugaye za su kai su ga hallaka.

  7. Ubangiji yana bincike adalai, amma ransa yana ƙi mugaye da masu son rikici.

  8. Ya Ubangiji, da hannunka ka cece ni daga irin mutanen nan, daga mutanen duniyan nan waɗanda ladarsu yana a wannan rayuwa ne. Kakan cika yunwan waɗanda kake so; ’ya’yansu suna da isashe suna kuma ajiyar wadata wa ’ya’yansu.

  9. Amma ni, cikin adalci zan ga fuskarka; sa’ad da na farka, zan gamsu da ganin kamanninka.

  10. Azaban mugu da yawa suke, amma ƙaunar Ubangiji marar ƙarewa kan kewaye mutumin da ya dogara gare shi.

  11. gama za a kakkarya ikon mugaye, amma Ubangiji zai riƙe mai adalci.

  12. Kwanakin marasa zarge suna sane ga Ubangiji, kuma gādonsu zai dawwama har abada.

  13. A lokutan masifu ba za su yanƙwane ba; a kwanakin yunwa za su sami a yalwace.

  14. Amma mugaye za su hallaka, Abokan gāban Ubangiji za su zama kamar kyan gonaki, za su ɓace, za su ɓace kamar hayaƙi.

  15. Mugaye kan yi rance ba sa kuma biya, amma masu adalci suna bayar hannu sake;

  16. waɗanda Ubangiji ya sa wa albarka za su gāji ƙasar, amma waɗanda ya la’anta, za a kore su.

  17. Ka dubi marasa zargi, ka lura da adali; akwai sa zuciya domin mutum mai salama.

  18. Amma za a hallaka dukan masu zunubi; za a yanke sa zuciya ta mugaye.

  19. Allah ya shirya masu kaɗaici a cikin iyalai, ya jagorance ’yan kurkuku da waƙoƙi; amma ’yan tawaye suna zama a ƙasa mai zafin rana.

  20. Zabura ta Asaf. Tabbatacce Allah mai alheri ne ga Isra’ila, ga waɗanda suke masu tsabta a zuciya.

  21. Amma game da ni, ƙafafuna suna gab da yin santsi; tafin ƙafana ya yi kusan zamewa.

  22. Gama na yi kishin masu girman kai sa’ad da na ga cin gaban da masu mugunta suke yi.

  23. Ba sa yin wata fama; jikunansu lafiya suke da kuma ƙarfi.

  24. Ba sa shan wata wahalar da sauran mutane ke sha; ba su da damuwa irin na ’yan adam.

  25. Saboda girman kai ya zama musu abin wuya; tā da hankali ya zama musu riga.