Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Wicked

724 ayoyi · 18 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zai sha dafin maciji; sarar maciji mai dafi za tă tashe shi.

  2. Ba zai ji daɗin koguna da rafuffuka masu kwarara da zuma da madara ba.

  3. Dole yă ba da abin da ya yi gumi kafin yă samu, ba zai ci ba; ba zai ji daɗin ribar da ya samu daga kasuwancinsa ba.

  4. Gama ya ci zalin talakawa ya bar su cikin wahala; ya ƙwace gidajen da ba shi ya gina ba.

  5. “Ba shakka ba zai samu abin da yake ƙoƙarin samu ba, dukiyarsa ba za tă cece shi ba.

  6. Ba abin da ya ragu da zai ɗauka; arzikinsa ba zai dawwama ba.

  7. Yana cikin samun arziki, ɓacin rai zai auka masa; ƙunci mai ƙarfi zai zo masa.

  8. Lokacin da ya cika cikinsa, Allah zai zuba fushinsa a kansa, zai daddaka shi.

  9. Ko da yake yana guje wa makamin ƙarfe, kibiya mai bakin tagulla za tă huda shi.

  10. Zai zāre ta daga bayansa, tsinin zai fita daga hantarsa; tsoro zai cika shi;

  11. duhu kawai yake jiran dukiyarsa. Wutar da ba a fifita ba za tă cinye shi ta kuma ƙona duk abin da ya rage a tentinsa.

  12. Sammai za su fallasa laifinsa; duniya za tă yi gāba da shi.

  13. Ambaliyar ruwa za tă tafi da gidansa, ruwaye masu gudu a ranar fushin Allah.

  14. Abin da Allah zai sa yă faru da mugu ke nan, gādon da Allah ya ba shi ke nan.”

  15. Don me mugaye suke rayuwa har su tsufa, suna kuma ƙaruwa da iko?

  16. Suna ganin ’ya’yansu suna girma, suna ganin jikokinsu suna tasowa a kan idanunsu.

  17. Gidajensu suna zama cikin lafiya ba ruwansu da fargaba. Kuma Allah ba ya ba su horo.

  18. Shanunsu ba sa fasa haihuwa; suna haihuwa ba sa yin ɓari.

  19. Suna aika ’ya’yansu kamar garke; ’ya’yansu suna guje-guje da tsalle-tsalle.

  20. Suna rera da kayan kiɗa na ganga da garaya; suna jin daɗin busar sarewa.

  21. Suna yin rayuwarsu cikin arziki kuma su mutu cikin salama.

  22. Duk da haka suna ce wa Allah, ‘Ka rabu da mu.’ Ba ma so mu san hanyoyinka.

  23. Wane ne Maɗaukaki har da za mu bauta masa? Wace riba za mu samu ta wurin yin addu’a gare shi?

  24. Amma arzikinsu ba a hannunsu yake ba saboda haka ba ruwana da shawarar mugaye.

  25. “Duk da haka, sau nawa fitilar mugu take mutuwa? Sau nawa bala’i yake auka masa, ko Allah ya taɓa hukunta mugu cikin fushi?