- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Promises of God
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
Zan albarkaci duk wanda ya albarkace ka, in kuma la’anci duk wanda ya la’anta ka, dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka.”
Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.
Ka zauna a wannan ƙasa na ɗan lokaci, zan kuwa kasance tare da kai, zan kuma albarkace ka. Gama zan ba da waɗannan ƙasashe gare ka da kuma zuriyarka. Zan kuma cika rantsuwar da na yi wa mahaifinka Ibrahim.
Zan sa zuriyarka ta yi yawa kamar taurari a sararin sama zan kuwa ba su dukan waɗannan ƙasashe, ta wurin ’ya’yanka kuma za a albarkaci dukan al’umman duniya,
Zuriyarka za tă zama kamar ƙurar ƙasa, za ka kuma bazu zuwa yamma da kuma gabas, zuwa arewa da kuma kudu. Dukan mutanen duniya za su sami albarka ta wurinka da kuma ta wurin ’ya’yanka.
Sa’an nan Yaƙub ya yi addu’a, “Ya Allah na mahaifina Ibrahim, Allah na mahaifina Ishaku. Ya Ubangiji kai da ka ce mini, ‘Koma ƙasarka zuwa wurin danginka, zan kuma sa ka yi albarka.’
Amma ka riga ka faɗa, ‘Tabbatacce zan sa ka yi albarka. Zan kuma sa zuriyarka su zama kamar yashin teku da ba a iya ƙirgawa.’ ”
Bari Ubangiji, Allahn kakanninku yă ƙara yawanku sau dubu, yă kuma albarkace ku yadda ya yi alkawari!
Yanzu da Ubangiji Allahnku ya ba ’yan’uwanku hutu kamar yadda ya yi alkawari, sai ku koma gidajenku a ƙasar da Musa bawan Ubangiji ya ba ku a Urdun.
“Yanzu na kusa barin fuskar duniyan nan. Kun sani da dukan zuciyarku, da dukan ranku cewa, Ba ko ɗaya daga cikin alkawuran da Ubangiji Allahnku ya yi, da bai cika ba. Kowane alkawari ya cika; ba ko ɗaya da bai cika ba.
Sa’ad da kwanakinka suka ƙare, za ka huta tare da kakanninka, zan tā da zuriyarka, na cikinka, zan kuma sa mulkinsa ya kahu.
Shi zai gina gida domin Sunana, zan kuwa kafa gadon sarautarsa har abada.
“Yabo ya tabbata ga Ubangiji, wanda ya ba wa mutanensa hutu kamar dai yadda ya yi alkawari. Babu magana guda da ta kāsa cika cikin dukan alkawaransa masu kyau da ya yi ta wurin bawansa Musa.
“Yanzu kuwa, Ubangiji, bari alkawarin da ka yi game da bawanka da gidansa yă kahu har abada. Yi kamar yadda ka yi alkawari,
Ya Ubangiji, kai ne Allah! Ka yi alkawari abubuwa masu kyau wa bawanka.
Ƙaunarsa marar ƙarewa ta ɓace ke nan har abada? Alkawarinsa ya kāsa ke nan a dukan lokaci?
Sai na yi tunani, “Zan yi roƙo saboda wannan, shekarun da Mafi Ɗaukaka ya miƙa hannunsa na dama.”
Ka ce, “Na yi alkawari da zaɓaɓɓena, na rantse wa Dawuda bawana,
cewa ‘Zan kafa zuriyarka har abada in kuma sa kursiyinka yă tsaya daram dukan zamanai.’ ” Sela
Sau ɗaya ba ƙari, na rantse da tsarkina, ba kuwa zan yi ƙarya wa Dawuda ba,
cewa zuriyarsa za tă ci gaba har abada kuma kursiyinsa zai dawwama a gabana kamar rana;
Ya tuna da alkawarinsa mai tsarki da ya ba wa bawansa Ibrahim.
Ubangiji ya ce, “Yanzu fa ku zo, bari mu dubi batun nan tare, Ko da zunubanku sun yi ja kamar garura, za su zama fari kamar ƙanƙara; ko da sun yi ja kamar mulufi, za su zama kamar ulu.
Sa’ad da kuka bi ta ruwaye, zan kasance tare da ku; sa’ad da kuka bi ta koguna, ba za su kwashe ku ba. Sa’ad da kuke tafiyata cikin wuta, ba za tă ƙone ku ba; harsunan wutar ba za su ƙone ku ba.
Ku tunashe ni abin da ya riga ya wuce, bari mu yi muhawwara wannan batu tare; ku kawo hujjarku na nuna rashin laifinku.