Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Promises of God: Fulfilled in Christ
Ayoyi game da Fulfilled in Christ
Ya tā mana ƙahon ceto a gidan bawansa Dawuda
(yadda ya yi magana tun tuni ta wurin annabawansa masu tsarki),
cewa zai cece mu daga abokan gābanmu daga kuma hannun dukan waɗanda suke ƙinmu
don yă nuna jinƙai ga kakanninmu, yă kuma tuna da alkawarinsa mai tsarki,
rantsuwar da ya yi wa mahaifinmu Ibrahim,
“Daga zuriyar mutumin nan ne Allah ya kawo wa Isra’ila Mai Ceto Yesu, kamar yadda ya yi alkawari.