Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Mercy of God

102 ayoyi · 36 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama kamar yadda sammai suke can bisa duniya, haka girmar ƙaunarsa yake wa masu tsoronsa;

  2. Amma daga madawwami zuwa madawwami ƙaunar Ubangiji tana tare da waɗanda suke tsoronsa, adalcinsa kuma tare da ’ya’yansu,

  3. Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  4. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  5. Ba gare mu ba, ya Ubangiji, ba gare mu ba amma ga sunanka yă sami ɗaukaka, saboda ƙaunarka da amincinka.

  6. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  7. Bari Isra’ila yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  8. Bari gidan Haruna yă ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  9. Bari waɗanda suke tsoron Ubangiji su ce, “Ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.”

  10. Ku gode wa Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  11. Duniya ta cika da ƙaunarka, ya Ubangiji; ka koya mini ƙa’idodinka.

  12. Ya Isra’ila, sa zuciya ga Ubangiji, gama tare da Ubangiji akwai ƙauna marar ƙarewa kuma tare da shi akwai cikakkiyar fansa.

  13. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  14. Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  15. Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  16. Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  17. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  18. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  19. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  20. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  21. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  22. Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  23. Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  24. Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  25. Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce.