Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Mercy of God: Is part of his character
Ayoyi game da Is part of his character
Sai Ubangiji ya wuce a gaban Musa, ya yi shela ya ce, “Ni ne Ubangiji Allah mai tausayi, mai alheri, mai jinkirin fushi, cike da ƙauna da aminci,
nakan nuna ƙauna wa dubbai, nakan kuma gafarta mugunta, tawaye da zunubi. Amma ba na barin mai laifi, ba tare da na hore shi ba; nakan hukunta ’ya’ya da jikoki har tsara ta uku da ta huɗu saboda laifin iyaye.”
Suka ƙi su saurare ka, suka kāsa tuna da mu’ujizan da ka aikata a cikinsu. Suka yi taurinkai, cikin tawayensu kuma suka naɗa shugaba don su koma bautarsu. Amma kai Allah ne mai gafartawa, mai alheri da jinƙai, mai jinkirin fushi, mai yalwar ƙauna. Saboda haka ba ka yashe su ba,
kuma cewa kai, ya Ubangiji, mai ƙauna ne. Tabbatacce za ka sāka wa kowane mutum bisa ga abin da ya yi.”
Sai ya yi addu’a ga Ubangiji ya ce, “Ya Ubangiji, ba irin abin da na faɗa ke nan ba tun ina gida? Wannan ne ya sa na yi ƙoƙarin tserewa zuwa Tarshish. Ai, na sani kai Allah ne mai alheri da tausayi, mai jinkirin fushi da cikakkiyar ƙauna, kai Allah ne mai dakatar da nufinka na yin hukunci.
Sai Ubangiji ya ce, “Ai, wannan kuringa ta tsira dare ɗaya ta kuma ɓace kafin dare na biyu, ba ka yi wata wahala dominta ba, ba kai ne ka sa ta yi girma ba, duk da haka ranka ya ɓace saboda ita.
Ashe, ba dole ne in ji tausayin babban birnin nan Ninebe mai mutum sama da dubu ɗari da ashirin (120,000) marasa alhaki, da kuma dabbobi masu yawa ba?”
Yabo ya tabbata ga Allah, da Uban Ubangijinmu Yesu Kiristi, Uba mai tausayi, da kuma Allah na dukan ta’aziyya,