Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Mercy of God: Everlasting

30 ayoyi · 36 fannoni

Ayoyi game da Everlasting

Tace bisa littafi
  1. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama shi nagari ne; ƙaunarsa madawwamiya ce.

  2. Zan ci gaba da ƙaunarsa har abada, alkawarina da shi ba zai taɓa fasa ba.

  3. Yabi Ubangiji. Yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  4. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi; ƙaunarsa madawwamiya ce har abada.

  5. Ku yi godiya ga Ubangiji, gama nagari ne shi. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  6. Ku yi godiya ga Allahn alloli. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  7. Ku yi godiya ga Ubangijin iyayengiji. Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  8. Gare shi wanda shi kaɗai yake aikata abubuwan banmamaki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  9. Wanda ta wurin ganewarsa ya yi sammai, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  10. Wanda ya shimfiɗa duniya a kan ruwaye, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  11. Wanda ya yi manyan haskoki, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  12. Rana don tă yi mulkin yini, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  13. Wata da taurari kuma don su yi mulkin dare; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  14. Gare shi wanda ya kashe ’ya’yan fari Masar Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  15. Ya kuma fitar da Isra’ila daga cikinsu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  16. Da hannu mai ƙarfi da hannu mai iko; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  17. Gare shi wanda ya raba Jan Teku biyu Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  18. Ya kawo Isra’ila ta tsakiyarsa, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  19. Amma ya share Fir’auna da mayaƙansa cikin Jan Teku; Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  20. Gare shi wanda ya bi da mutanensa cikin hamada, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  21. Wanda ya buge manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  22. Ya karkashe manyan sarakuna, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  23. Sihon sarkin Amoriyawa Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  24. Da kuma Og sarkin Bashan, Ƙaunarsa madawwamiya ce.

  25. Ya kuma ba da ƙasarsu gādo, Ƙaunarsa madawwamiya ce.