Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shoes

36 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. cewa ba zan karɓi kome da yake naka ba, ko zare ko maɗaurin takalma, don kada ka ce, ‘Na azurta Abram.’

  2. Allah ya ce, “Kada ka zo kusa, tuɓe takalmanka, gama inda kake tsaye, wuri ne mai tsarki.”

  3. Ga yadda za ku ci shi, ku yi ɗamara, takalma kuwa a ƙafafunku, kuna riƙe da sandunan tafiya a hannunku. Ku ci shi da gaggawa; Bikin Ƙetarewa ne na Ubangiji.

  4. sai gwauruwan nan, matar ɗan’uwansa tă haura wurinsa a gaban dattawa, tă tuɓe takalminsa guda, ta tofa masa miyau a fuska, tă ce, “Haka za a yi ga mutumin da zai ƙi kafa gidan ɗan’uwansa.”

  5. Za a kira zuriyarsa a Isra’ila Iyalin da aka tuɓe masa takalmi.

  6. Shekaru arba’in da na jagorance ku cikin hamada, tufafinku ba su yage ba, haka kuwa takalman da suke a ƙafafunku.

  7. Madogaran ƙofofinka za su zama ƙarfe da tagulla, ƙarfinka kuma zai zama daidai da kwanakinka.

  8. Shugaban rundunar sojojin Ubangiji ya amsa ya ce, “Ka cire takalmanka, gama wurin da kake tsaye, mai tsarki ne.” Sai Yoshuwa ya cire takalmansa.

  9. Suka sa tsofaffin takalman da suka sha gyara, suka sa tsofaffin tufafi. Dukan abincinsu na tafiya ya bushe ya yi fumfuna.

  10. Waɗannan salkuna kuma da muka cika ruwan inabi, sababbi ne amma duba yadda suka yayyage. Tufafinmu da takalmanmu duk sun yayyage don doguwar tafiya.”

  11. (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.)

  12. Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa.

  13. Amma Dawuda ya ci gaba yana hawan Dutsen Zaitun, yana kuka yayinda yake tafiya; kansa a rufe, kuma babu takalma a ƙafafunsa. Dukan mutanen da suke tare da shi suka rufe kawunansu suna ta kuka yayinda suke haurawa.

  14. “Yanzu fa, kai kanka ka san abin da Yowab ɗan Zeruhiya ya yi mini. Abin da ya yi wa shugabanni biyun nan na mayaƙan Isra’ila, wato, Abner ɗan Ner, da Amasa ɗan Yeter. Ya kashe su, ya kuma zub da jininsu a lokacin salama sai ka ce a fage yaƙi, da wannan jini ya yi ɗamara a gindinsa, ya kuma sa takalma a ƙafafunsa.

  15. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirarin nasara.”

  16. Mowab shi ne kwanon wankina, a kan Edom zan jefa takalmina; a bisa Filistiya zan yi kirari cikin nasara.”

  17. Ƙafafunki a cikin takalma kyakkyawa ne, Ya diyar sarki! Tsarin ƙafafunki sun yi kamar kayan ado masu daraja, aikin hannun gwanin sassaƙa.

  18. A wannan rana Ubangiji zai ƙwace abin da suke taƙama da shi, mundayensu, ɗankwalin kansu da abin wuyansu,

  19. a wannan lokaci Ubangiji ya yi magana ta wurin Ishaya ɗan Amoz. Ya ce masa, “Tuɓe tsummokin da kake saye da su, da kuma takalman da ka sa a ƙafafu.” Ya kuwa yi haka, yana yawo tsirara kuma ba takalma a ƙafa.

  20. Sa’an nan Ubangiji ya ce, “Kamar dai yadda bawana Ishaya ya yi ta yawo tsirara kuma ba takalmi a ƙafa shekara uku, a matsayin alama da shaida a kan Masar da Kush,

  21. Ɗauki dutsen niƙa ki niƙa gari; ki kware lulluɓinki. Ki ɗaga fatarinki ki bar ƙafafunki tsirara, ki kuma yi ta ratsa cikin rafuffuka.

  22. Kada ka yi gudu har ƙafafunka su zama ba takalma maƙogwaronka kuma ya bushe. Amma sai ka ce, ‘Ba amfani! Ina ƙaunar baƙin alloli kuma dole in bi su.’

  23. Na rufe ki da rigar da aka yi wa ado na kuma sa miki takalman fata. Na sa miki riga ta lilin mai kyau na kuma rufe ki da riguna masu tsada.

  24. Ka yi nishi shiru; kada ka yi makoki saboda matacciyar. Ka naɗa rawaninka ka kuma sa takalmanka a ƙafa; kada ka rufe sashen fuskarka daga ƙasa ko ka ci abincin da masu kuka sukan ci.”

  25. Za ku naɗa rawunanku a kai ku sa takalmanku a ƙafafunku. Ba za ku yi kuka ko makoki ba amma za ku lalace saboda zunubanku ku kuma yi ta yin nishi.