Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shoes

36 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ga abin da Ubangiji ya ce, “Saboda zunubai uku na Isra’ila, har guda huɗu ma, ba zan fasa hukunta su ba. Don sun sayar da adalai waɗanda suka kāsa biyan bashinsu. Sun kuma sayar da matalauta waɗanda bashinsu bai ma kai ko kuɗin bi-labi ba.

  2. mu sayi matalauta da azurfa masu bukata kuma da takalmi, mu sayar da alkamar haɗe da yayi.

  3. “Ina muku baftisma da ruwa domin tuba. Amma wani yana zuwa a bayana wanda ya fi ni iko, wanda ko takalmansa ma ban isa in ɗauka ba. Zai yi muku baftisma da Ruhu Mai Tsarki da kuma wuta.

  4. kada ku ɗauki jaka don tafiya, ko ƙarin riga, ko takalma ko sanda; domin ma’aikaci ya cancanci hakkinsa.

  5. Yesu ya ce, “Ku zo, ku bi ni, ni kuwa zan mai da ku masuntan mutane.”

  6. Ku sa takalma, amma ban da riga fiye da waɗanda kuka sa.

  7. Kada ku ɗauki jakar kuɗi, ko jaka, ko takalma. Kada ma ku gai da kowa a kan hanya.

  8. “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa.

  9. Shi ne mai zuwa bayana, wanda ko igiyar takalmansa ma ban isa in kunce ba.”

  10. Sa’an nan mala’ikan ya ce masa, “Ka sa rigunarka da takalmanka.” Bitrus kuwa ya sa. Mala’ikan ya faɗa masa cewa, “Ka yafa mayafinka ka bi ni.”

  11. shirin kai bisharar salama yă zama kamar takalmi a ƙafafunku.