Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Seeking God

88 ayoyi · 64 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’ad da mutane suka ce muku ku nemi shawarar ’yan bori da masu sihiri, waɗanda suke shaƙe murya har ba a jin abin da suke faɗi, bai kamata mutane su nemi shawara daga Allahnsu ba? Me zai sa ku nemi shawara daga matattu a madadin masu rai?

  2. Amma mutanen ba su juyo wurin wanda ya buge su ba, balle su nemi Ubangiji Maɗaukaki.

  3. Raina yana marmarinka da dare; da safe kuma raina yana son ganinka. Sa’ad da hukunce-hukuncenka suka sauko duniya, mutanen duniya kan koyi adalci.

  4. Kaiton waɗanda suka gangara zuwa Masar don neman taimako, waɗanda suke dogara ga dawakai, waɗanda suke dogara ga yawan kekunan yaƙinsu da kuma a girman ƙarfin mahayan dawakansu, amma ba sa dogara ga Mai Tsarkin nan na Isra’ila, ko ya nemi taimako daga Ubangiji.

  5. Duba a cikin littafin Ubangiji ka kuma karanta. Babu wani a cikin waɗannan da ya ɓace, babu ko ɗaya da ba ta da abokiya. Gama bakinsa ne ya ba da umarni, Ruhunsa kuma zai tara su wuri ɗaya.

  6. Ban yi magana asirce ba, daga wani wuri a ƙasar duhu ba; ban faɗa wa zuriyar Yaƙub, ‘Ku neme ni a banza ba.’ Ni, Ubangiji maganar gaskiya nake yi; na furta abin da yake daidai.

  7. Ku nemi Ubangiji tun yana samuwa; ku yi kira gare shi tun yana kusa.

  8. Gama kowace rana suna nemana; suna marmarin sanin hanyoyina, sai ka ce al’ummar da take yin abin da yake daidai ba ta kuma yashe umarnan Allahnta ba. Sun nemi shawarwaran da suke daidai daga gare ni suna kuma marmari Allah ya zo kusa da su.

  9. Za ku neme ni ku kuwa same ni sa’ad da kuka neme ni da dukan zuciyarku.

  10. Ubangiji mai alheri ne ga waɗanda suke da bege a cikinsa, ga kuma wanda yake neman shi;

  11. Sai na juya wurin Ubangiji Allah na roƙe shi ta wurin addu’a da koke-koke, cikin azumi, ina saye da tsummoki, na kuma zauna a cikin toka.

  12. Na yi addu’a ga Ubangiji Allahna na furta laifina. “Ya Ubangiji, mai alfarma da kuma Allah mai banrazana, wanda yake cika alkawarinsa na ƙauna ga duk wanda ya ƙaunace shi ya kuma kiyaye dokokinsa,

  13. Sa’an nan zan koma wurina sai sun yarda da laifinsu. Za su kuma nemi fuskata; cikin azabansu za su nace da nemana.”

  14. Ku shuka wa kanku adalci, ku girbe ’ya’yan jinƙai marar ƙarewa, ku kuma nome ƙasar da ba a nome ba; gama lokaci ne na neman Ubangiji, sai ya zo ya zubo adalci a kanku.

  15. Ga abin da Ubangiji ya ce wa gidan Isra’ila. “Ku neme ni ku rayu;

  16. Ku nemi Ubangiji ku kuma rayu, ko kuwa zai ratsa yă share gidan Yusuf kamar wuta; zai cinye Betel kuwa ba zai sami wanda zai kashe ta ba.

  17. “Zan miƙa hannuna gāba da Yahuda da kuma dukan mazaunan Urushalima. Zan datse raguwar Ba’al daga wannan wuri, da sunayen firistocin gumaka da na marasa sanin Allah,

  18. waɗanda suka rusuna a kan rufin ɗaki don su yi sujada ga rundunar taurari. Waɗanda suka rusuna suka kuma yi rantsuwa da sunan Ubangiji suke kuma rantsuwa da sunan Molek.

  19. Waɗanda suka juya daga bin Ubangiji, ba sa kuma neman Ubangiji ko su nemi nufinsa.”

  20. Ku nemi Ubangiji, dukanku ƙasashe masu tawali’u, ku da kuke yin abin da ya umarta. Ku nemi adalci da tawali’u; mai yiwuwa ku sami mafaka a ranar fushin Ubangiji.

  21. “Gama ya kamata leɓunan firist su kiyaye ilimi, ya kamata kuma mutane su nemi umarni daga bakinsa, domin shi ne manzon Ubangiji Maɗaukaki.

  22. “Duba, zan aika manzona, wanda zai shirya hanya a gabana. Sa’an nan a farat ɗaya Ubangiji wanda kuke nema zai zo haikalinsa. Manzon alkawari, wanda kuke sa zuciya kuwa zai zo,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  23. Da farko dai, ku nemi mulkin Allah da kuma adalcinsa, za a kuwa ba ku dukan waɗannan abubuwa.

  24. “Ku roƙa za a ba ku; ku nema za ku samu; ku ƙwanƙwasa za a kuwa buɗe muku ƙofa.

  25. Da mala’ikun suka bar su, su suka koma sama, sai makiyayan suka ce wa juna, “Mu je Betlehem mu ga wannan abin da ya faru, wanda Ubangiji ya sanar mana.”