Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Samuel

135 ayoyi · 22 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.” Suka ce, “I, shi ne shaida.”

  2. Sama’ila ya ce, “Me ke nan ka yi?” Shawulu ya ce, “Sa’ad da na ga mutane suna watsewa, kai kuwa ba ka zo cikin lokaci ba, ga Filistiyawa kuma suna taruwa a Mikmash,

  3. sai na yi tunani cewa, ‘Yanzu Filistiyawa za su gangaro su fāɗa mini a Gilgal, ga ni kuma ban riga na nemi nufin Ubangiji ba.’ Shi ya sa ya zama mini tilas in miƙa hadaya ta ƙonawa.”

  4. Sama’ila ya ce, “Ka yi wauta da ba ka bi umarnin da Ubangiji Allahnka ya ba ka ba. Da ka yi haka da Ubangiji ya tabbatar maka da sarautar Isra’ila har abada.

  5. Amma yanzu, masarautarka ba za tă dawwama ba, Ubangiji ya riga ya sami wani wanda zuciyarsa ke ƙauna, ya naɗa shi shugaban mutanensa gama ba ka bi umarnin Ubangiji ba.”

  6. Sama’ila ya tashi daga Gilgal ya tafi Gibeya a ƙasar Benyamin. Shawulu kuma ya ƙidaya mutanen da suke tare da shi, yawansu ya kai wajen mutum ɗari shida.

  7. Da Dawuda ya gudu ya tsere, sai ya tafi wurin Sama’ila a Rama ya gaya masa dukan abin da Shawulu ya yi masa. Da shi da Sama’ila suka tafi Nayiwot suka zauna a can.

  8. Sama’ila ya rasu, sai dukan Isra’ila suka taru suka yi makoki saboda shi. Suka binne shi a gidansa a Rama. Sai Dawuda ya gangara zuwa cikin Jejin Faran.

  9. Sama’ila dai ya riga ya rasu, dukan Isra’ila suka yi makokinsa suka binne shi a garinsa a Rama. Shawulu kuma ya kori duk masu duba da masu maitanci daga ƙasar.

  10. Filistiyawa suka tattaru suka yi sansani a Shunem. Shawulu ya tattara dukan Isra’ila suka yi sansani a Gilbowa.

  11. Da Shawulu ya ga sojojin Filistiyawa sai ya ji tsoro, ya firgita ƙwarai.

  12. Ya nemi nufin Ubangiji amma bai sami amsa daga wurin Ubangiji ko ta wurin mafarki, ko ta wurin Urim, ko ta wurin annabawa ba.

  13. Shawulu ya ce wa fadawansa, “Ku nemo mini wata mace mai duba domin in tafi wurinta in yi tambaya.” Suka ce, “Akwai guda a En Dor.”

  14. Sai Shawulu ya sa waɗansu tufafi ya ɓad da kama, shi da waɗansu mutum biyu suka tafi wurin matar da dare, ya ce mata, “Ki yi mini duba ta hanyar sihiri, ki hawar mini duk wanda zan faɗa miki.”

  15. Amma matar ta ce masa, “Tabbatacce ka dai san abin da Shawulu ya yi, ya karkashe masu duba da masu maitanci a ƙasar. Me ya sa kake sa mini tarko, don ka sa a kashe ni?”

  16. Shawulu ya rantse mata da Ubangiji. Ya ce, “Muddin Ubangiji yana a raye, ba za a hukunta ki a kan wannan ba.”

  17. Sai matar ta ce, “Wa kake so in hauro maka?” Sai ya ce, “Ki hauro mini da Sama’ila.”

  18. Da matar ta ga Sama’ila sai ta yi ihu da ƙarfi ta ce wa Shawulu, “Me ya sa ka ruɗe ni? Kai ne Shawulu!”

  19. Sai sarki ya ce mata, “Kada ki ji tsoro. Me kika gani?” Matar ta ce, “Na ga wani kurwa tana fitowa daga ƙasa.”

  20. Ya ce, “Yaya kamanninsa yake?” Ta ce, “Wani tsoho sanye da taguwa ne yake haurawa.” Shawulu ya gane cewa Sama’ila ne, sai ya rusuna da fuskarsa har ƙasa.

  21. Sama’ila ya ce wa Shawulu, “Don me ka dame ni, ta wurin hauro da ni?” Shawulu ya ce, “Ina cikin babban damuwa ce, Filistiyawa sun fāɗa mini, Allah kuma ya juya mini baya. Bai amsa mini, ko ta mafarki, ko kuma ta annabawa ba, saboda haka na kira ka don ka gaya mini abin yi.”

  22. Sama’ila ya ce, “Don me kake tambayata bayan Ubangiji ya rabu da kai? Ya zama maƙiyinka?

  23. Ubangiji ya cika abin da ya yi magana ta wurina. Ubangiji ya fizge mulki daga hannunka, ya ba maƙwabcinka Dawuda.

  24. Gama ba ka yi biyayya ga Ubangiji ba, ba ka zartar da hukuncinsa mai zafi a kan Amalekawa ba. Saboda haka Ubangiji ya yi maka haka yau.

  25. Ubangiji zai ba da Isra’ila da kuma kai ga Filistiyawa, gobe kuwa da kai da ’ya’yanka za ku kasance tare da ni. Ubangiji kuma zai ba da sojojin Isra’ila a hannun Filistiyawa.”