Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Samuel: His integrity as judge and ruler

8 ayoyi · 22 fannoni

Ayoyi game da His integrity as judge and ruler

  1. Sama’ila ya ce wa Isra’ilawa duka, “Na saurari abubuwan da kuka faɗa mini, na kuma naɗa muku sarki.

  2. Yanzu kuna da sarki a matsayin shugaba, ni kuwa na tsufa har da furfura, yarana maza kuma suna tare da ku. Na yi shugabancinku tun ina yaro.

  3. Ga ni a gabanku. Idan na yi wani abin da ba daidai ba sai ku faɗa a gaban Ubangiji, da gaban sarkin da ya keɓe. Ko na taɓa ƙwace saniya ko jakin wani? Ko na taɓa cuce wani, ko in danne hakkinsa? Ko na taɓa cin hanci daga hannun ɗayanku? Idan na taɓa yi ɗaya daga cikin waɗannan, sai ku faɗa mini, zan kuwa mayar masa.”

  4. Suka ce, “Ba ka cuci ko danne hakkin kowa ba, ba ka ƙwace kome daga hannun kowa ba.”

  5. Sama’ila ya ce musu, “Ubangiji yă zama shaida a kanku, shafaffensa kuma yă zama shaida a wannan rana cewa ba ku same ni da wani laifin kome ba.” Suka ce, “I, shi ne shaida.”

  6. Musa da Haruna suna cikin firistocinsa, Sama’ila yana cikin waɗanda suka kira bisa sunansa; sun kira ga Ubangiji ya kuwa amsa musu.

  7. Sai Ubangiji ya ce mini, “Ko da Musa da Sama’ila za su tsaya a gabana, zuciyata ba za tă komo ga mutanen nan ba. Ka kore su daga gabana! Su tafi!

  8. Me kuma zan faɗa? Ba ni da lokacin da zan ba da labari a kan Gideyon, Barak, Samson, Yefta, Dawuda, Sama’ila, da kuma annabawa,