Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Samuel: Consecrated to God before his birth

7 ayoyi · 22 fannoni

Ayoyi game da Consecrated to God before his birth

  1. Ta yi ta cewa, “Ya Ubangiji Maɗaukaki. In har ka dubi baƙin cikin baiwarka, ka tuna da ni, ba ka kuma manta da baiwarka ba, amma ka ba ta ɗa, ni ma zan miƙa shi ga Ubangiji dukan rayuwarsa, aska kuwa ba za tă taɓa kansa ba.”

  2. Hannatu kuwa ba tă bi su ba. Ta gaya wa mijinta cewa, “Sai bayan na yaye yaron, zan kai shi in miƙa shi a gaban Ubangiji, yă kuma kasance a wurin koyaushe.”

  3. Bayan ta yaye shi, sai ta ɗauki yaron tare da bijimi bana uku, da mudun gari, da salkan ruwan inabi, ta kawo su a gidan Ubangiji a Shilo.

  4. Bayan an yanka bijimin, sai suka kawo yaron wurin Eli.

  5. Sai ta ce masa, “Ranka yă daɗe, ba ka gane ni ba? Ai, ni ce matar da ta taɓa tsayawa a gabanka, tana addu’a ga Ubangiji.

  6. Wannan yaron ne na roƙa daga wurin Ubangiji, ya kuwa ba ni abin da na roƙa daga gare shi.

  7. Saboda haka, na ba da shi ga Ubangiji muddin ransa, zai zama na Ubangiji.” A can kuwa ya yi wa Ubangiji sujada.